Al-Shabaab na ci gaba da kai hare-hare | Labarai | DW | 05.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shabaab na ci gaba da kai hare-hare

Duk da nasarar da dakarun kasar Somaliya ke cewa sun samu a baya-bayan nan a kan 'yan kungiyar al-Shabaab, har yanzu kungiyar na ci gaba da kai farmaki.

Wani dan kunar bakin wake ya tada bama-baman da ke makare cikin motarsa a kusa da ayarin sojojin Somaliya da Amirka ta bai wa horo a Mogadishu babban birnin kasar. A cewar wani jami'in 'yan sanda na Somaliyan akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayin wannan hari da tuni kungiyar al-Shabaab da ke gwagwarmaya da makamai a kasar ta dauki alhakin kaiwa. Wani jami'in sojan Somaliyan Kaftin Mohamed Hussein ya ce mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu a harin wanda aka kai shi a hanyar filin sauka da tashin jiragen sama na Mogadishu, fararen hula ne da ke tafiya a gefen titi. A cewar kakakin ma'aikatar tsaron Somaliyan Mohamed Yusuf gwamnati ta san da shirin kai wannan hari, kuma dan kunar bakin waken ya tada bam din ne a yayin da jami'an tsaro suka biyo shi a kokarin da suke na kama shi. Irin wadannan hare-hare daga kungiyar ta al-Shabaab dai ba wani bakon abu ba ne a Somaliya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal