al-Assad na son kura ta lafa a Syriya
March 1, 2016Shugaban Bashar al-Assad na Syriya ya yi alkwarin tsayawa a kan kafafunsa don ganin cewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Amirka da Rasha ta ci gaba da aiki a kasarsa. Cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin mallakar gwamnatin Jamus wato ARD, al-Assad ya yi tayin yafe wa duk 'yan bindigan Syriya da za su ajiye makamansu.
A halin yanzu dai gwamnatin Syriya da kuma bangaren tawaye na ci gaba da zargin junansu da rashin mutuntu yarjejeniyar tsagaita wuta sau da kafa. Ko da ita ma Rasha sai da ta bayyana cewar fadar mulkin ta Damascus ta saba wa wannan yarjejeniya so 15 a yankunan Homs da Aleppo a cikin sa'o'i 24 na bayan-bayannan.
Sai dai shugaban na Syriya ya ci ba kamshi gaskiya a ciki, inda ya ce "'Yan tawaye ne suka saba wa wannan yarjejeniya tun sa'o'i farko bayan da ta fara aiki. Alhali dakarun gwamnati sun yi iya kokarinsu don ganin cewa sun mutuntata."