1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai ƙarancin tallafi a Afirka ta Tsakiya

February 28, 2014

A karon farko cikin watanni biyu ayarin motocin kayayyakin tallafi sun shiga Bangui babban birnin ƙasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda waɗanda yaƙi ya tarwatsa ke matuƙar buƙata

https://p.dw.com/p/1BHUE
Lebensmittelverteilung im Lager
Hoto: DW/S. Schlindwein

Kimanin mutane dubu 250 suka tsere daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya zuwa ƙasashen dake maƙotaka da su, a yayin da wasu milliyan ɗaya kuma a cikin ƙasar suka rasa matsugunnensu suna samun mafaka a majami'u da makarantu. A yanzu haka dai ƙungiyoyin tallafin ƙasa da ƙasa sun ce fiye da rabin al'ummar ce ke dogaro da tallafin da suke bayarwa amma kuma suna fiskantar ƙalubale wajen samar da kayyakin da ake buƙata sakamakon rashin motocin ɗaukar kaya.

Wannan ne karon farko a tsukin watanni biyu da ayarin motocin kayayyakin tallafi ke zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Tare da rakiyar motocin soji, trailoli fiye da ɗari masu maƙare da kayan abinci suka shiga birnin Bangui. A yayin da dakarun Faransa dake ɗauke da makamai ke baje a kan titunan ƙasar domin tabbatar da tsaro. Bisa dalilai na tsaro dai sai da trailolin suka shafe mako guda kan iyakar ƙasar da Kamaru kafin suka samu suka shiga ƙasar ranar laraba 25 ga watan Fabrairu.

Wuraren da waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita ke samun mafaka

Yanayin dake kasancewa ke nan a sansanonin marasa matsugunnen, inda ɗruruwan su ke samun mafaka a filin jirgin sama, Cocuna, makarantu da masallatai, sai dai yanayin da suke ciki abin takaici e domin babu ruwan sha, babu wurin kewayewa kuma mafi mahimmanci akwai ƙarancin abin kaiwa bakin salati.

A yanzu haka dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta shigar da abinci kuma mutane irin su Herve Hesse sun sami buhunan garin masara. Shi dai Herve Hesse yana da yara biyu kuma ya fara fargaban cewa wataƙila ɗansa dake da shekaru biyar, na fama da rashin lafiya saboda ƙarancin abinci mai gina jiki

Familie von Herve Hesse
Iyalin Herve HesseHoto: DW/S. Schlindwein

"Wannan ne karo na uku da muke samu abinci a tsukin watanni biyu, a wannan karon ma mun sami tabarmi da tukwanen girki, wannan ya tallafa mana sosai domin mu da kanmu bamu iya samu. Sai dai wanda ake kawo mana ba ya isa. Ina da yara biyu mu huɗu ke nan, yau mun sami kilo biyar na wake, kilo 30 na garin masara da mai litre guda da rabi, wannan tsanani ya yi mana makonni biyu, idan muka haɗa da rogo ko wani abu, amma yawancinmu ba mu kuɗin ɓatarwa, saboda haka muna kira ga al'ummar ƙasa da ƙasa da su tura mana abubuwa kamar suga da madara"

Kason al'ummar dake fama da yunwa

Kusan rabin al'ummar jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar wadda ke da yawan milliyan huɗu da rabi na dogaro ne da tallafi, kuma wannan adadi na ƙaruwa ne saboda tun bayan ɓarkewar rikicin, manoma basu iya zuwa gona bare ma su girbo shukan da suka yi, kuma kayayyakin masarufin dake Bangui sun yi kaɗan, kuma abin da ma aka samu, ya yi tsada sosai, ba'a biya albashi ba kuma bankuna na rufe, ƙalubalen dai ya yi yawa a cewar Alexis Marciarelli na shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya:

"Babban ƙalubalen shi ne samar da abinci, tsakanin makonni biyun da suka gabata tonne 85 kaɗai muka kai Bangui, sai ka ji kamar wannan na da yawa amma dubban mutane ne muke ƙoƙarin ciyarwa, wannan kwanaki uku kaɗai zai yi. Matsalar hanyar Kamaru ce, domin ita ce kaɗai za a iya bi wajen fita da shiga, kuma a watan Janairu an rufe iyakar na tsawon makonni uku, kuma tun lokacin, ayarin motoci uku suka shiga, kuma wannan ba zai isa ba idan har muna so kowa ya samu"

Lastwagen kommen in Bangui an
Sai motoci sun yi aƙalla mako guda a Kamaru kafin su shiga BanguiHoto: DW/S. Schlindwein

Ƙorafin ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya

Hukumar tallafi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ko ɗaya ba ta shirya wa wannan bala'in ba, kuma idan har ba a iya samar da abincin yadda ya kamata ba za a shiga wani mawuyacin hali

"Mun yi wani bincike inda muka gano cewa kashi 90 cikin 100 na manoman ƙasar ba su da iri wannan kaɗai zai iya janyo babban bala'i, mun riga mun fara gai alamu tamowa musamman a yara. Babu wanda ya san tsawon lokacin da wannan rikicin zai ɗauka, ko sadda ma tattalin arziƙin zai farfaɗo, ko ma lokacin da mutane za su koma aiki har su sami kuɗi kasuwanni su cika, a bara kawai mutane fiye da milliyan ɗaya ke fama da yunwa tun ma kafin rikicin ya ɓarke. Tsakanin nan da watan Ogosta muna buƙatan sama da dola milliyan 100 sai dai ba ma yawan kuɗin bane matsalar, sadda za mu same su a hannu ne"

A watan Afrilu za a shiga damina, inda dole manoma su fara shuka amma ko hakan zai yiwu? ita ce babbar tambayar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe