Aikin tattara sakamakon zabe a kasar Mali | Siyasa | DW | 12.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Aikin tattara sakamakon zabe a kasar Mali

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta dukufa domin bayyana sakamakon zabe zagaye na biyu nan zuwa ranar Laraba

Bayan zaben shugaban kasa zagaye na biyu cikin kwanciyar hankali da lumana, yanzu al'umar kasar Mali sun shiga jiran sakamako.

Aikin tattara sakamakon zabe ya rataya akan Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, tare da taimakon ofishin ministan cikin gida.

Ko wace jiha daga jihohin kasar gaba daya na tattara sakamakonta kamin daga bisani ta tura shi zuwa hukumar tsakiya.

A yankin Bamako wannan aiki na gudana a fadar gwamnatin jiha.Georges Togo shine gwamnan jihar Bamako yayi karin haske game da yadda aikin ke wakana:

"Ko wane lardi ya na tattara sakamakon da ya samu a cikin runfunansa gaba daya, sannan tare da rakiyar 'yan sanda a kawo su nan kai tsaye ba tare da an tsaya ko ina ba."

Ibrahim Boubacar Keita Presidential candidate Ibrahim Boubacar Keita speaks at a news conference during Mali's presidential election in Bamako, July 28, 2013. Voters in Mali headed to the polls on Sunday in a presidential election it is hoped will the provide a fresh start to a country divided by a coup and a war in its desert north. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: ELECTION POLITICS)

Ibrahim Boubacar Keita

Bayan kawo takardun a cibiyar babban birni, wakilan 'yan takara da na Hukumar Zabe da kuma na gwamnati bisa sa idon alkalai, na bin dindinkin ko wane sakamako domin kaucewa kuskure.

A cewar gwamnan jihar Bamako a wannan karo bisa ga dukan alamu za a samu sakamakon karshe cikin gaggauwa.Ya bada dalilai:

"A zagayen farko akwai 'yan takara 27, kenan tantance kuri'un da kowa ya samu aiki ne mai wahala.A yanzu 'yan takakar guda biyu ne rak.A zagayen fako mun fara daren Lahadi mu ka kare ranar Laraba da yamma.A yanzu ina ga alamun aikin ya fi sauri".

A wani mataki na hakikance cewa zaben na Mali ya gudana cikin adalci kungiyoyi masu zaman kansu na kasar gaba daya, sun girka wata hada ka, domin bi sau ada kafa.Ibrahima Sangho shine shugaban hadin gwiwar kungiyon masu zaman kansu.Ya baiyana irin rawar da suka taka wajen nasara zaben:

" Misali idan wakilan da muka aika a cikin kasa domin sa ido su ka gano wata runfar zabe da ta buda ba a nan take za mu buga waya ga a hukumar da yaunin runfar ya rataya kanta domin daukar mataki.Hakan ya taimaka matuka gayya, wajen magance kura-kurai da dama.Fa'idar wannan shine warware matsala take-yanke a maimakon a saka mata ido sai bayan kwanaki uku a hiddo sanarwa domin baiyana ta.Wannan mataki na riga kafi shine mu ke kira sa ido na kishin kasa."

Soumaïla Cissé auf dem Weg zu einer Pressekonferenz in Bamako Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 29. Juli 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Bamako, Mali

Soumaïla Cissé

Duk da cewar Hukumar zabe ta yi nisa wajen tattara sakamakon amma ta ki cewa uffan game da dan takara da ke sahun gaba.Nan da ranar Laraba mai zuwa, ake sa ran za ta baiyan sakamakon wucin gadi na karshe.

A nasu bangare ,'yan takara biyu da suka fafata a zagaye na biyu wato Ibrahim Bubakar Keita da Sumaila Cisse ,sun yi kira ga magoya bayansu su kasancewa masu ladabi da biyyaya ga duk sakamakon da zai fitto, hakan kuwa ba karamar narasa ce ba, ga demokradiyar kasar Mali.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin