1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin kungiyar Kids Club Kampala na taimaka wa yara marasa galihu

May 2, 2013

Da zaran an ambaci unguwar marasa galihu ba abin dake zuwa hankalin mutun in banda miyagun ayyuka , talauci, da shan miyagun kwayoyi da matasa ke yi domin kauce wa tunanen mawuyacin halin da suke ciki.

https://p.dw.com/p/18Q6B
Hoto: Bastian Schnabel

 DW ta dauki yini guda tana nazari akan aikin da wata kungiya ke yi a unguwar Katanga, wadda unguwa ce ta marasa galihu a birnin kamplalan kasar Uganda , domin fid da yara daga mawuyacin hali na rayuwa

Kids Club Kampla wata kungiya ce da ke aiki a wata unguwar marasa galihu a birnin Kampla na kasar Uganda. Wannan unguwa unguwa ce da aka kafa a bayan ginin jam'iar Makerere mai tazarar kilomita biyar da tafiyar mota daga tsakiyar birnin Kampla. A kowace ranar asabar ce yaran masu da shekarunsu na haifuwa suka kama  daga shida zuwa 15 ke haduwa a cikin ginin cocin Jesus Salvation Centre inda suke koyon raye-raye da kade kade. Kuma a hakika  kowanensu na jin dadin kasancewa mambobi na wannan kungiya

Wa ke tallafa wa Kids Club Kampala da kudi?

Kungiyar Kids Club Kampala wadda kungiya ce mai zaman kanta Samuel Wambayo da Oliver Barker ne suka assasa ta a shekarar 2009. Kuma tana aiki ne a unguwannin marasa galihu dabam-dabam da ke birnin Kampala domin taimaka wa yara da adadindsu ya yi sama da dubu hudu. Manufar kungiyar dai ita ce yi wa yaran jagora ga zama manya kwarai na gobe masu fahimta  ga rayuwa  ba tare da waiwayen mawuyacin halin da suka taba fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum ba.  Ko da yake tallafin da wannan kungiya ke samu bai taka kara ya karya ba, to amma  Wambayo kan yi hamdallah da dan abin da yake samu daga al'uma domin tafiyar da shirye-shiryen kungiyar. Shi kansa a lokacin da yake  yaro sai da ya sayar da wasu kadarori nasa wato kaza guda da dan akwatin rediyo domin samun kudin tallafa wa matakin karshe  na iliminsa na firaimare. A don haka ne a yanzu a matsayinsa na  shugaban Kids Club Kamplala yake zaman ganau ba ji yau ba  game da halin rayuwa da mazauna unguwannin marsaa galihun ke tsintar kansu a ciki.

 "Kamata ya yi mutun yayi kokarin samar da kauna  saboda cewa idan ka je unguwar  Katanga  za ka fahimci  cewa unguwa ce ta marasa galihu da ke fama rikce-rikice a ko da yau she. A da za ka tarar da yara suna  fada da junansu. To amma yanzu mun tara  da dama daga cikinsu a wuri daya kuma yanzu ba ka kace na ce.  Muna tabbatar da cewa mun samar da yanayin nuna wa juna kauna tare kuma da yi musu jagora a rayuwa  saboda daukar mu da suke a matsayin abin koyi." Inji Wambayo

Afrika kommt Chronist der Winde Henning Mankell
Hoto: Deutsche Kammerphilharmonie Bremen/Jörg Sarbach

Kyeyuna Charles  malamin sa kai ne a fannin  koyar da waka . Ya ce burinsa shine ya ga kungiyar  yara mawakan ta shahara a koina cikin duniya.

"Ina jin dadin kasacewa tare da wadannan yara a duk sanda nike koyar da su wake. Ina son in basu horo na sana'a."

 Yaran sun gamsu da abin da ake koyar da su

Bayan kowane zama na  koyon wake yaran su kan zauna ne a kasa domin sauraron nasiha daga malamansu guda biyu . Ana  koyar da su muhimmacin kauce wa mugun aiki  da kuma muhimmacin yin bitar abin da aka karantar da su, da nuna biyayya ga iyaye da zama diya na gari da kuma ganin girman kowa babba da yaro.

Uganda Ehemalige Kindersoldatin
Hoto: picture-alliance/dpa

Da karfe biyar rabi na maraice ne  ake sallamar yaran  to amma Kiza Arafat ya ce yana begen ganin an kebe wani aji da za su rinka zuwa da rana a duk ranar Asabar. Ya kara da cewa yana kokarin jawo abokansa su shiga  wannan kungiya, yana kuma basu shawara mai kyau.

Ya ce:"  Ni kan yi kira gare su da su yi wa kansu zabi na kwarai saboda cewa mafi yawansu ba su ganin girman iyayensu  kuma suna barin gida su shiga watanagaririya."

Mawallafiya: Laila Ndida/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi