Aikin jin kai na matasa a watan Ramadan | BATUTUWA | DW | 21.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Aikin jin kai na matasa a watan Ramadan

Hadakar kungiyoyin zabin sonka na birnin Damagaram kusan 20 a karkashin Club des Jeunes Big Tempo sun gudanar da tarin ayyukan lada albarkacin azumin Ramadan, watan da a cikinsa Musulmi ke neman kusancin da ubangiji ta hanyar aikata alhairi kamar yadda addini ya umurta.

A dubi bidiyo 03:09

Matasan sun yaye kallabin tsarin a bankin katihu da adana Jini na birnin Damagaram CRTS, inda membobin kungiyoyin maza da mata suka yi tururuwa don ajjiye guziri mai yawa na Jini bisa la’akari da karuwar bukata da ake samu da zarar watan Azumi ya kama. 


Mata na sahun gaba na wadanda suka amsa kira don zuwa wannan aiki ma falala wanda sakayyasa na gurin ubangiji, kuma suna masu alfahari da samun dama ta su taimakawa ‘yan uwansu. 

Kungiyoyin matasa da dama ne dai suka zama tsintsiya madaurinki daya a karkashin tsarin, kuma za su share wata daya cur suna hidimta wa Musulmi baya ga gudunmawar kayan marmari har ma da ta suturar sakawa a ranar sallah wa marayu, mata masu yoyon futsari da kuma iyalai masu karamin karfin.