Ahuwa ga tsohon shugaban hukumar leƙen asiri na Sudan
July 10, 2013Talla
Ana dai tuhumar Salah Gos da laifin shirya wani juyin mulki domin kifar da gwamnatin Umar Hassan El-Beshir. Lauyan da ke kare tsohon jami'in ya ce an sako shi ne a kan ahuwar da shugaban ƙasar ya ke yi a kowace shekara idan watan azumi ya kama.
Salah Gos dai ya riƙe matsayin na shugaban hukumar leƙen asiri na Sudan kana mashawarcin shugaban ƙasar tun daga shekarun 2009 zuwa farkon shekarun 2011. An kuma cafke shi ne a cikin watan Otkoban da ya gabata aka kuma tsare bayan wani binciken da aka gudanar wanda ya gano cewar yana da hannu a cikin wani yunƙurin juyin mulkin da ya ci tura .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh