Afrika ta kudu ta nemi ganawa da Jami′in jakadancin Amirka. | Labarai | DW | 15.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afrika ta kudu ta nemi ganawa da Jami'in jakadancin Amirka.

Kasar Afrika ta kudu ta nemi ganawa da wani kusa a ofishin jakadancin Amirka dake kasar a yau litinin,don wani taron gaggawa akan furucin ‘batancin da shugaban kasar Amirka Donald Trump yayi akan kasashen Afirka .

Südafrika Präsdient Jacob Zuma (Reuters/S. Sibeko)

Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma

Wannan furuci na Trump ya yi matukar girgiza Kasashe da yawa a fadin duniya musamman ma kasashen Afrika da ya alakanta da kaskanci.

Furucin dai ya janyo Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Tarayyar  Afrika su zargi Trump da rura wutar wariyar launin fata a fakaice duk kuwa da cewar yayi amai ya lashe a cikin wani rubutu da ya kuma yi a shafinsa na Twitter.

Wata sanarwa da ta fito akan taron gaggawar, gwamnatin Afrika ta kudu ta bayyana cewar akwai bukatar dangantaka tsakanin Amirka da Afrika ta kudu ta zamo bisa fahimta da mutunta juna.

A wani ci gaban kuma, ita ma kasar Botswana ta nemi jakadanta dake kasar ta Amirka da ya tambayi Amirka ko kasarsu na cikin kasashen da Trump ya yi wa kudin goro.