Afrika ta Kudu: Matsalar ruwa a Cape Town
Sakamakon hasashen cewa za a fuskanci karancin ruwa a Cape Town cikin 'yan watanni, tuni aka fara takaita raba ruwan ga jama'a. Ko yaya mazauna birnin ke ji da wannan lamari?
Maraba da ruwan sama
Wata rana ta shudin launin sararin samaniya a Cape Town, inda karancin ruwan sama da janyewar madatsun ruwa suka jefa birnin cikin matsanancin matsalar ruwa. An dauki tsauraran matakan takaita raba ruwa, sai dai ta yi wu a rasa ruwa a birnin nan da watan Afrilu na 2018.
Kowanne digon ruwa yana da amfani
Wani mazaunin birnin ya sanya duro domin tara ruwan sama a gidansa da ke Cape Town. Idan ruwa ya dauke a famfo, kowanne dan kasa zai sami lita 25 ne kacal kwatankwacin galon 7 na ruwan sha a kowace rana a cibiyoyin ba da ruwa a fadin birnin.
Komai ya bushe
Hanyar da aka saba gani da korayen ciyayi a gefen kogi, a yanzu ta kasance lullube da ciyawa busasshiya. Tun tsakiyar 2017 aka haramta amfani da ruwan sha domin ban ruwan lambu. A kokari na alkinta ruwan karkashin kasa, birnin ya kuma hana haka rijiyoyin burtsatse domin ban ruwa.
Kirkiro sabunta ruwa domin kasuwanci
Wannan wurin wanke motoci a yankin wurin shakatawa na gabar kogi na amfani da dabarar sabunta ruwa da aka adana a cikin tanki wajen wanke motoci. A wannan hali na takaita ruwa, wajibi ne wuraren kasuwanci su rage amfani da ruwa da kashi 45 cikin 100, idan aka kwatanta da yadda suke amfani da ruwa a shekara ta 2015 ko kuma su fuskanci tara.
Bukatar tankunan ruwa ta karu
Wajen wani babban gida an inganta matakan adana ruwa. Ana iya ganin wasu tankuna da aka rubuta cewa an sayar da su. An takaita amfani da ruwa zuwa lita 87 ga kowane mutum guda a rana, Yayin da ranar da ruwan zai dauke ke gabatowa bukatar tankunan ruwa ta karu.
Ruwan teku a wuraren iyo da ninkaya
Wuraren iyo na jama'a a wuraren shakatawa na gabar kogi na ci gaba da gudana. Tafkunan ninkayar guda hudu an cika su da ruwan tekun Atlantika. Domin alkinta ruwan tekun. Masu gudanar da wurin shakatawar sun rufe fanfunan wanka na shawa.