Afrika ta Kudu: Boren dalibai kan kudin makaranta | Siyasa | DW | 05.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afrika ta Kudu: Boren dalibai kan kudin makaranta

Tun bayan da gwamnati ta kara kashi takwas cikin dari na kudaden da dalibai ke biya ne daliban manyan kwaleji suka fara boren

Tun bayan da ministan ilimi a kasar ta Afirka ta Kudu Blade Nzimande ya bayyana karin kashi bakwai cikin darin na kudin da dalibai ke biya an shiga rudani daliban na cewa an musu alkawari na ba karin kudin makaranta yanzu an karya.

A ranar Alhamis din nan jami'oi da abin yafi shafa su ne jami'ar Cape Town da ta Western Cape da ta Witwatersrand a Johannesburg da Nelson Mandela a Port Elizabeth.

Thato Mokoena mamba ne a kungiyar dalibai a jami'ar Wits da ke a birnin na Johannesburg kuma daya cikin masu zanga-zangar ya ce sun sha gallazawa a hannun jami'an tsaro.


 
Mun fara taho mu gama da jami'an 'yan sanda bayan da muka fito zanga-zanga muna wake-wake sun haumu da duka kuma muna ganin cewa dukkaninmu muna da dama ta tsayawa mu yi zanga-zanga dan 'yancinmu ne. 

 

Malaman dai na cewa ba sa goyon bayan gallazawar da ake wa dalibai, sai dai wadannan dalibai na son karatu ne kyauta, kuma mai inganci kamar yadda jami'oi ke fadi, sai dai a fadar Shirona Patel da ke magana da yawun jami'ar Witwatersrand a Johannesburg  a zantawa da DW hakan ba mai yiwuwa ba ne karatu kyauta saboda karancin kudi da suke fama da shi.

 

Dalibai na son karatu ba ta re da biyan kudi ba yanzu kuma suke so wannan ba abu ne mai yiwuwa ba sai dai nan da 'yan shekaru kuma a yanzu dalibai na yin amfani da kafafan sadarwa inda suke yi wa 'yan uwansu barazana abu ne da ba zamu lamunta ba.

 

Duka dalibai a kasar dai sun yi watsi da wannan kari wanda bayansa ma  Khutso Kganyago wata daliba cikin masu zanga-zangar ta ce ana kuma nuna musu banbanci a ingancin na karatu ma tsakanin daliban bakar fata da farar fata dan haka dole su yaki wannan dabi'a.

Dole mu hada kai mu zama tsintsiya madaukinki daya dole mu kalubalanci wannan mataki kasancewar ana nuna banci a fannin karatu farar fata daban bakar fata daban fararen fata na samun ilimi mafi inganci bayan kuwa dukanmu abu guda ne.

Wani gungun dalibai karkashin wasu 'yan fafutika da suka kira kansu da kungiyar "Dole kudin makaranta ya fado Kasa" sun shiga jami'ar Wits inda suka nemi da a rufe makarantar sai dai 'yan sanda sun fito don yin fito na fito da dalibai. Sai dai jami'ar ta bayyana cewa wasu dalibai na son komawa makaranta dan haka za su koma karatu a mako mai zuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin