1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan JAridun Jamus akan Afirka

January 29, 2021

A wannan makon daukacin jaridun Jamus sun mayar da hankali ne kan sabon nau'in cutar corona da yadda ta shafi tattalin arzikin nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3oaEX
Afrika Sambia Coronavirus Vorkehrungen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Mwiche

Idan muka fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi a karo na uku kasar Afirka ta Kudu ta haramta sayar da barasa a cikin kasar a mataki na dakile yaduwar annobar corona. Jaridar ta ce yanzu haka sabuwar annobar cutar na yaduwa a kasar a daidai lokacin da asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu sun kai makura na yawan marasa lafiya da za su iya karba. Ba a kuma san ranar da za a fara yi wa al'ummar allurar riga-kafin cutar ba. Al'ummar Afirka ta Kudu dai sun yi suna wajen yawan kwankwadar barasa, saboda haka haramcin dafawa ko sayarwa ko amfani da barasar babbar illa ce ga tattalin arzikin kasar musamman ga kamfanonin giya da otel-otel da ma daidaikun mutane masu sayar da barasar. Gidajen abinci da dama da mashaya tuni sun rufe tun bayan kafa dokar haramta amfani da barasar a Afirka ta Kudun. Yanzu haka dai wasu kamfanonin yin giya sun daukaka kara suna neman kotu ta soke dokar ko kuma akalla ta ba da izinin sayar da barasa don masu sha a gida.

Südafrika | SANDF Soldatin
Hoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Annobar corona na ci gaba da dora kasashe da dama ciki har da Zambiya kan turbar karayar tattalin arziki da rashin kudi, a cewar jaridar Neues Deutschland. Ta ce kamar a bangaren kiwon lafiya, tattalin arzikin kasashe da yawa na yankin kudancin duniya ya shiga mawuyacin hali. Jaridar ta ruwaito wani bincike kan basassuka a 2021 da ke cewa kasashe 132 matsalolin bashi suka kai musu iya wuya, karin kasashe takwas ke nan idan aka kwatanta da 2020. Zambiya ce kasar farko da matsalar rashin iya biyan bashi ta shafa sakamakon cutar corona. Tattalin arzikin kasar dai ya dogara ne a kan tagulla da take sayarwa kasashen ketare, amma sakamakon corona farashin jan karfen ya fadi kasa warwas a kasuwannin duniya.

Ita kuwa a labarin da ta buga kan corona a Afirka, jaridar Der Tagesspiegel cewa ta yi sahu na karshe a jerin masu jira. Jaridar ta ce a Afirka da wuya ka ji ana allurar riga-kafin corona, domin kasashe masu ci-gaban masana'antu sun kasance a sahun farko na wadanda ke samun alluran riga-kafin corona. Ta ce a tserereniyar da ake kan samun riga-kafin corona kasashe masu tasowa msamman na Afirka, sun zama 'yan kallo, dole su jira tsawon lokaci suna mafarkin samun na su kason. Rashin daidaito wajen samun riga-kafin abin damuwa ne da ya zama wajibi a gano bakin zaren magance shi.

Demokratischen Republik Kongo | Congo River
Hoto: Frans Lanting/picture alliance

A karshe za mu leka kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango inda jaridar Die Tageszeitung ta labarto cewa a karon farko wata sabuwar doka a Kwango za ta tabbatar da 'yancin wadanni 'yan asalin mazauna dazukan kurmin kasar. Jaridar ta ce wadannin dai sune tsirarun al'umma a Kwango da ba su da wata kariya, inda ake yawaita yi musu kisan gilla, kamar a ranar 13 ga watan Janerun nan an yi wa wadanni 46 kisan gilla a yankin Abembi da ke lardin Ituri na arewa maso gabacin Kwango. Shugaban kungiyar farar hula a Ituri ya kwatanta aika-aikara da kisan kare dangi. Yawan wadanni a Kwango ya kai dubu 600 zuwa dubu 700 kimanin kashi daya cikin 100 na al'ummar kasar. Ko da yake ana maraba da dokarfamma bisa al'ada kafa doka a Kwango ba ya nufin aiwatar da ita.