1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka za ta karbi bakuncin Obama

LateefaJune 26, 2013

A karon farko tun bayan darewarsa kan karagar mulki a shekara ta 2009, Shugaba Barack Obama na Amirka zai kai ziyarar tsahon mako guda a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/18wwy
Hoto: picture-alliance/dpa

A yau Laraba ne shugaban kasar Amirka Barack Obama zai fara wata ziyarar aiki a nahiyar Afirka. Ziyarar tasa dai ita ce karo na biyu da zai kai nahiyar a matsayinsa na shugaban kasar Amirka bayan takaitacciyar ziyarar da ya kai kasar Ghana da Masar tun farkon hawansa kan karagar mulki.

Tun da aka zabi Barack Obama a matsayin shugaban Amirka bakar fata na farko a shekara ta 2008, al'ummar nahiyar Afirka da suke ganin Obama na da alaka da su a matsayinsa na dan asalin kasar Kenya, suka sanya burika da dama da suke tunanin Amirkan zata taimaka musu wajen cimma wadannan burika nasu.

Sai dai kuma da dama na ganin Obama bai yi wani abin azo a gani ba a fannin dangantakarsa da nihiyar da take zaman tushensa na asali, wanda hakan ya sanya a yanzu wasu ke ganin ziyarar tasa bata da wani muhimmancin gaske, kamar yadda wani dan jarida a kasar Salo Issa Mansary ya ce bai ga wani canji daga Shugaba Obama ba tun da ya samu darewa kan karagar mulki a shekara ta 2009 kawo yanzu.

African Economic Outlook 2013 - Publikum African Economic Outloook 2013
Ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka a shekara ta 2013Hoto: DW/C. Vieira

Ya ce " Idan ka dubi nahiyar Afirka zaka ga cewa bai yi wani abun azo a gani ba wajen ci gaban yankin, musamman a fannin tsaro da kuma dorewar mulkin dimokaradiyya. Ya kafa wata rundunar tsaro ta Amirka da ke kula da nahiyar Afirka,mai suna "AFRICOM" amma shalkwatar rundunar na kasar Jamus mai makon a Afirka. Munga zai kai ziyara zuwa Tanzaniya da Afirka ta Kudu, munji zai kai ziyara kasar Guinea, munji kuma abubuwan da yake wajen kawo karshen rikicin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu. Amma a kwai bukatar bada gudunmawar da ta fi wannan".

An dai shirya wannan ziyara ta Obama ne da nufin ta yi duba ga wasu daga cikin matakan da duniya ke dauka wajen magance fatara a tsakanin al'umma a kasashe masu tasowa. Wani Farfesa kan al'amuran da suka shafi kasa da kasa a Jami'ar Washington David Shinn ya bayyana na sa ra'ayin kan wannan ziyara ta Barack Obama.

Afrikanische Union feiert 50. Jubiläum
Kungiyar Tarayyar Afirka AU na bikin cikarta shekaru 50 da kafuwa.Hoto: AFP/Getty Images

Ya ce " Abinda ya faru shine a lokacin mulkinsa na farko bai mayar da hankali kan matsalolin da suke addabar nahiyar Afirka ba, ina ga yanzu ya na so ya gyara abun da ya yi a baya ne shi ya sanya ya shirya kai ziyara nahiyar tun farkon hawansa kan karagar mulki a karo na biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa Obama zai kwashe tsahon kwanaki bakwai yayin wannan ziyara tasa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu