Afirka ta Tsakiya: Shirin zabe zagaye na biyu | Labarai | DW | 25.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Tsakiya: Shirin zabe zagaye na biyu

Kotu a birnin Bangui ta bada sakamakon karshe na zaben shugaban kasar zagaye na farko inda a halin yanzu aka samu tabbacin wadanda za su kara a zagayen na biyu.

'Yan takara Anicet-Georges Dologuélé da Faustin-Archange Touadéra ne za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar wanda zai gudana a ranar 31 ga watan nan na Janairu. A zagaye na farko dai da ya gudana a ranar 30 ga watan Disamba, Dologuélé ne ya samu mafi yawan kuri'u na kashi 23,74, yayin da Touadera ya zo na biyu da kashi 19,05 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. Da ya ke magana da DW Dolegele ya ce abun da ke jiransu a nan gaba ba karami ba ne.

"Akwai abubuwa da dama ta ya kamata a yi, domin sanin kanku ne kasa ce wadda komai sai an sake, kuma a sahun bukatu, akwai batun dawo da cikeken tsaro, zaman lafiya da kuma sasanta 'yan kasa, dukanninsu ne za su bada damar farfado da tattalin arzikin kasar."