Afirka ta Kudu ta fice daga Kotun ICC | Labarai | DW | 21.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu ta fice daga Kotun ICC

Afirka ta Kudu ta sanar da ficewa daga kotun kasa da kasa da ICC, bayan da a baya ta yi barazanar yin hakan shekara guda bayan cece kucen da ya biyo bayan rishin kame Shugaba kasar Omar El-Béchir na Sudan.

 Wannan mataki dai na Afirka ta Kudu na ficewa daga Kotun ta kasa da kasa, na a matsayin wani babban kalubale ga kotun mai cibiya a birnin Hague na kasar Holland. Kamar yadda aka tanadi  tsarin ficewar, hukumomin na Pretoria sun sanar wa babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya wannan mataki na su a rubuce, a cewar ministan harkokin wajen kasar ta Afirka ta Kudu Michael Masutha.

A shekara ta 2003 ne dai kotun ta kasa da kasa ta ICC ta soma aikinta wadda kuma ke a matsayin kotun farko da aka kafa da ke bin diddigin masu aikata manyan laifuka musamman ma na yaki, a inda ake aiwatar da kashe-kashen mutane barkatai.

Sai dai daga cikin bincike goma da kutun ta kaddamar, guda takwas dukannin sun shafi kasashen Afirka ne kwai, inda a baya ma kungiyar Tarayyar Afirka ta soki lamirin wannan mataki na nuna banbanci da kotun ke yi a cewarta.