Afirka ta Kudu: Garanbawul a majalisar ministoci
March 31, 2017Talla
Bayan da aka shafe tsawon kwanaki ana yada jite-jite kan wannan batu, sai da yammacin ranar Alhamis ce dai Shugaba Zuma ya aiwatar da sauye-sauye mai girma a majalisar ministocinsa.
Ya nada sabbin ministoci 10 da mataimakansu 10. Wannan mataki ya haifar da faduwar canjin a kasar bisa fargabar abun da zai iya biyo bayan wannan sauyi.
Shugaba Zuma dai ya mika mukamin ministan kudin kasar ga wani na hannun damansa mai suna Malusi Gigaba, wanda a baya ya ke a matsayin ministan cikin gida.
An dai jima ana samun takun saka tsakanin Zuma da ministan na shi na kudi Gordhan, wanda a ranar Litinin da ta gabata shugaban ya nemi da ya dawo maza-maza daga wata ziyara da ya ke yi a Birtaniya.