Afirka ta Kudu: ANC na zaben shugabanninta
December 16, 2017Talla
A taron da jam'iyyar ke yi a birnin Johannesburg ana sa ran takara za ta yi zafi, tsakanin mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa da Nkosazana Dlamini-Zuma tsohuwar matar Jacob Zuma kana tsohuwar shugabar kwamitin kungiyar tarrayar Afirka. Wannan zabe dai na zuwa daf da lokacin da jam'iyyar ta ANC ake zargin shugabanninta da laifin cin hanci.