Afirka ta Kudu: ANC na shan kaye a zabe
August 6, 2016Talla
Daga cikin wuraren da jam'iyyar ta DA ta samu nasara har da babban birnin kasar Pretoria sai dai ya zuwa yanzu ba a kai ga samun sakamakon zaben a Johannesburg. Masu aiko da rahotannin dai na cewar daga dan abinda aka samu a wasu mazabun da ke Johannesburg wanda shi ne birni mafi girma a kasar, jam'iyyun biyu na yin kankankan. Za dai a samu kamalallen sakamakon zaben ne da misali hudu agogon GMT. Wannan dai shi ne karon farko da jam'iyyar ANC da ke rike da madafun iko ta samu koma baya a zabuka da aka gudanar a kasar tun bayan da aka kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar.