1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Afirka ta Kudu ta ba da sammacin kamo Zuma

Gazali Abdou Tasawa LMJ
February 4, 2020

Wata kotun birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu ta ba da a wannan Talata sammacin kamo tsohon shugaban kasar Jabob Zuma bayan da a jiya Litinin ya ki bayyana a gabanta.

https://p.dw.com/p/3XFTJ
Südafrika Prozess gegen Jacob Zuma in Durban
Hoto: Reuters/N. Bothma

Wata kotun birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu ta ba da a wannan Talata sammacin kamo tsohon shugaban kasar Jabob Zuma bayan da a jiya Litinin ya ki bayyana a zaman shari'ar da za a soma yi masa kan zargin karbar rashawa ta kudi kimanin Euro dubu 242 a wata kwangilar cinikin makamai ta kimanin miliyan dubu uku na Euro da kasar ta bai wa kamfanin Thales na Faransa a shekara ta 1999 a lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa.

 Sai dai kotun ta ce sammacin zai soma aiki daga ranar shida ga watan Mayu, ranar da za ta yi zamanta na biyu kan shari'ar idan har ya ki ya bayyana a gabanta. Lauyoyin tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu mai shekaru 77 a yau, sun bayar da uzurin cewa ba ya lafiya shi ya sa bai bayyana a gaban kotun ba. Sai dai kotun ta ce tana jiran a gabatar mata da hujjojin da ke tabbatar da rashin lafiyar tasa.