1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Johnny Clegg ya yi fafutuka a Afirka ta Kudu

Abdourahamane Hassane
July 17, 2019

Al'umma da shugabannin a Afirka ta Kudu na nuna alhini tare da tunawa da shahararan mawakin nan da ya rasu Johnny Clegg wanda ya taka rawa wajen yaki da nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3MDiR
Johnny Clegg und Band
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce har kullum za su rika tunawa da Johnny Clegg saboda fafutukar da ya yi ta yaki da nuna wariyar launin fata. An haifeshi a Birtaniya amma kuma ya rungumi al'adun kabilar Zulu wanda ya rika yin waka da harshen. Johnny Clegg ya rasu yana da shekaru 66 bayan ya yi fama da ciwon Cancer.