Afirka ta Kudu: Abinci mai cutarwa
Kusan rabin mutanen Afirka ta Kudu suna fama da matsalar kiba, musamman talakawa da ke rayuwa da abincin tafi da gidanka. Yana da arha amma babu lafiya kamar wajen cin abinci na Hillbrow da ke birnin Johannesburg.
Karuwar abincin tafi da gidanka a Afirka ta Kudu
A unguwannin marasa galihu, akwai abincin da ake kira "Kota" da galibin mutane tsoffi da yara ke saya. Akwai araha. Ana gwada kudin gwargwadon yawan abin da aka zuba. Abincin Kota ya kunshi dankalin Turawa da burodi gami da wasu kayayyaki.
Cika ciki da kudi kalilan
Amma Kota ya bambanta da gina jiki. A unguwannin marasa galihu, mutane suna kokarin rage kashe kudi. Haka masu sayar da Kota. Abincin mai kitse bai sauya ba. A shekarar da ta gabata Afirka ta Kudu ta yi fama da cutuka masu yaduwa, inda mutane 183 suka halaka saboda saka abin da bai dace ba cikin abinci.
Talauci da rashin abinci mai gina jiki
Abinci masu karancin kayan gina jiki na saka kiba, ga sukari da gishiri. Wannan matsala ce da ke yaduwa a Afirka ta Kudu kamar a birnin Johannesburg tamkar sauran kasashe masu tasowa. Irin wannan abinci kan janyo kiba. Abin da ke haifar da cutukan sukari, sankara da cutar zuciya. Wadannan cutuka ke haifar da mutuwar rabin masu karfi a jiki a Afirka ta Kudu.
Araha amma guba
Abinci maras gina jiki na da araha. A wannan babban shagon da ake kwana, ana sayar kilo daya na nama da aka sarrafa Euro uku. Abubuwan da ya kunsa: Nama da aka sarrafa na alade da kaza kashi 46 cikin 100. Saura kuma ruwa da sitati da wasu sinadarai.
Garin masara
"Abin da ake sayarwa cikin hanzari ke nan" in ji wani manejan kantin kayan abinci. Garin masara da gurguru sun samu karbuwa ga talakawa. Ana samu a gidaje da yawa. Mutane kuma kan sayi madara da sukari. A manyan shaguna da ke unguwannin masu hannu da shuni ana samun kayan abinci masu gina jiki. Amma da tsada.
Tuwo - kan haya da gida
Tuwo abincin kullum ga talaka. A gida aka yi ko a kan hanya in ji Thema Masuku wani mai saya. Tuwo da nama, ko yaushe mutane kan iya saya. Mutane ba sa da masaniya kan rashin abubuwa masu gina jiki, gami da muhimmancin sinadaran a jikin mutane.
Sabon yanayin cin abinci
A kasashe masu tasowa da dama, hanyar cin abinci ta sauya a shekarun da suka gabata: Mutane suna kara cin abinci da aka sarrafa a kamfani. A kasashe da dama ana nuna abinci tamkar wanda aka saba. Lamarin ya shafi kusan daukacin mutane.
Hadari na karuwa
Cutar sukari da bugun jini da kuma hawan jini ba kasafai ake gani a Afirka ba a baya. Amma kayan abinci masu kitse, gishiri da sukari kan janyo cutukan. A Afirka ana samun yaduwar cutukan. Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce zuwa shekara ta 2030, za su shiga gaba wajen kashe mutane.
Ganye - amma kalilan
"Ko mutane sun sayi ganye suna sauya hanyar amfani da shi." In ji Thandi Puoane na Jami'ar Westkapp. A wani bincike ta gano cewa ana amfani da alayyawo da timatir ko kabeji mai araha wanda zai kara kiba. Ana kuma saka wasu sinadarai. Abinci mai gina jiki sai ya zama guba.
Zabin abinci da ba yawa
"Mama Dombolo" wajen cin abinci a kontaina a Hillbrow. Akwai abinci guda tuwo da nama da miya. Kana ana samun dafa-duka irin na Afirka. Babu shakka marasa galihu suna zuwa cin abincin sosai wadanda suke sa da kiba.