Afirka: Rashin tabbas ga ba wa masu jego kariya a wurin aiki | Zamantakewa | DW | 09.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Afirka: Rashin tabbas ga ba wa masu jego kariya a wurin aiki

Wasu kasashen Afirka ciki har da Ruwanda sun bullo da tsare-tsare da ke zama abin koyi don ganin an kawar da wannan matsala.

Kimanin iyaye mata miliyan 830 ne a fadin duniya yanzu haka ke fuskantar kalubale na kariya a wuraren aikinsu a lokacin da suke hutu na haihuwa. Wasu kasashen Afirka sun yunkuro don ganin an kawar da wannan batu.

Kimanin kashi 80 cikin 100 na matan da ke fuskantar wannan matsala ta rashin samun kariya da ma tallafi daga wuraren aikinsu yayin da suke hutun haihuwa na zaune a kasashen Afirka da nahiyar Asiya. Ko da yake dai bisa ga binciken da kungiyar kwadago ta duniya ta gudanar kasashe irin su Maroko da Mali da Jamhuriyar Benin da kuma Burkina Faso sun fita zakka, sai dai su din ma akwai 'yan matsaloli nan da can kasancewar kudin hutu kawai suke biya. Laura Addatim wata mai bincike ce da ke aiki da kungiyar kwadago ta duniya ILO.

"Idan aka duba alkaluman da muka fidda a shekara ta 2014 za a ga cewar kasashe da aka gudanar da bincike kansu a Afirka sun nemi a biya masu jego kudade yayin da suke hutun haihuwa to sai dai tsarin bai da kyau na a zo a gani kamar yadda ake da shi a kasar Ruwanda wadda ke bada tallafi sosai ga mace da ke hutun haihuwa."

Barazanar rasa aiki bayan hutun jego

Mata da dama na kokawa kan irin wariyar da suke fuskanta lokacin da suke shirin tafiya hutun haihuwa da ma lokacin da suke hutun, musamman idan aka zo biyan wani hakki nasu baya.

Kenia Nairobi Frauen im Büro

Kusan a dukkan kasashen Afirka kamfanoni kawai ke daukar nauyin biyan kudin hutu ga mata masu hutun haihuwa

To sai dai wadannan matsaloli ba a nan suka tsaya ba. Guda daga cikin wadda ta fi ci wa matan tuwo a kwarya ita ce barazana da suke fuskanta ta rasa aikin baki dayansa duba da irin aiyyukan da yawa-yawan aikin da mata ke yi a kasashen Afirka. Venantino Karanja Mwangi da ke shugabantar wata cibiya mai zaman kanta a birnin Nairobin Kenya na daga cikin masu nuna damuwa kan wannan matsala.

"Idan ana magana ta uwa da yaranta musamman ma sabuwar haihuwa, iyaye mata kan so su dau dogon lokaci wajen zama tare da su. Wasu da dama ba su damu da kudin da za su samu ba, don sun fi ganewa su kasance da yaransu. Sam ba sa sanya idanu kan abin da gwamnati za ta basu ko da kuwa rabin abin da ya kamata su samu ne. Abin da suka fi damuwa da shi ne ko za su samu damar komawa bakin aiki nan gaba."

Koyi da tsarin kasar Ruwanda zai samar da mafita

Wannan hali da ake ciki dai yanzu haka ya sanya kungiyoyin mata da ma na kwadago da ke kasashen duniya daban-daban neman hukumomi da su tallafa wa ma'aikatu da kamfanoni wajen biyan wani kaso na kudin hutu da wasu hakkoki na matan da ke hutun haihuwa.

Senegal Kaloack Frau mit Kopftuch am Rechner

Mata a Afirka na aiki a fannoni daban daban

Wannan kira dai na zuwa ne daidai lokacin da wasu kasashe suka dukufa wajen yin 'yan gyare-gyare da nufin kasancewa kan godabe guda da kasar Ruwanda, wadda a iya cewa ita ce ke da tsari mafi kyau idan ana magana ta mata da masu zuwa hutun haihuwa. Laura Addatim ta kungiyar kwadago ta duniya ILO ta ce:

"Kasashe kamar Angola da Mozambik da Cote D'Ivoire sun fara yunkuri wajen fidda tsari irin wanda Ruwanda ke da shi da nufin ganin gwamnati ta dauki nauyi na biya masu juna biyu kudin hutun haihuwa maimako nwuraren da suke yin aiki. Wannan tsari ne mai kyau, sai dai a halin yanzu ba ya saurin da ya kamata."

Yanzu haka dai da dama na zuba idanu kan yadda lamura za su kasance a wadannan kasashe da Laura Addatim ta lissafa da ma irin matakan da sauran kasashe za su dauka da nufin kyautata wa iyaye mata da ke son tafiya hutu na haihuwa a kasashen da ke Afirka.