1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
March 5, 2021

A wannan makon batun garkuwa da mutane a Najeriya da raguwar samun masu kamuwa da annobar coronavirus a Afirka ta Kudu sun mamaye jardun Jamus a sharhunansu kan nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3qFoP
Nigeria | Zamfara | Schülerinnen Freilassung
'Yan matan makarantar Jangebe bayan an ceto su daga 'yan bindigaHoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

Jaridar Die Tageszeitung ta rubuta labarinta mais taken "Sabuwar annoba a Najeriya: Garkuwa da mutane masu yawa". Ta cigaba da cewar, an saki yara mata 'yan makarantar jihar Zamfara wajen 279 da aka sace. Sai annobar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na cigaba da addabar sassan Najeriya.

Da sanyin safiyar ranar Talatar ne ce dai, aka ceto 'yan matan da misalin karfe hudu na safe, inda kai tsaye aka kai su zauren majalisar dokokin jihar da ke Gusau. Da farko dai gwamnan jihar Bello Mutawalle ya ce akwai karin wasu 'yan matan 38 da basu dawo ba, amma daga bisani aka tabbatar da cewar adadin daliban da aka sace daga makarantar 'yan matan ta Jangebe da ke Khr Talata Mafara 279 ne.

Nigeria Hunderte Mädchen in Zamfara entführt
Dakunan kwanan dalibban Jangebe Hoto: Kola Sulaimon/AFP

A ranar Juma'a da rana tsaka ne dai wasu gungun mutane da aka ce sun kai 100, suka afkawa makarantar tare da kwashe 'yan matan bayan sun harbe mai gadi. Yara matan sun shaidar da yadda suka yi ta tafiya da kafa zuwa cikin jeji, inda babu ruwan sha mai kyau balle abincin arziki. 

Kamar dai yadda ya kasance a jihar Naija da ke makwabtaka makonni biyu da suka gabata, inda aka sako dalibai da malamansu wajen 42 da akayi garkuwa da su bayan tattaunawar sulhu da biyan kudin diyya.

Sace mutane da garkuwa da su domin neman kudin fansa dai ba sabon abu ba ne. A yankin Naija Delta mai albarkatun mai an sha sace ma'aikatan kamfanonin mai na ketare domin karbar kudin fansa.

Annobar COVID-19 ta fara raguwa

Impfkampagne in Südafrika
Dan kasar Afirka ta Kudu na rigakafiHoto: Siphiwe Sibeko/AP Photo/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine sharhi ta rubuta game da nasarar samun raguwar masu kamuwa da cutar coronavirus a kasar Afirka ta Kudu. Jaridar ta ce, tsawon makonni kenan ake samun raguwar sabbin masu corona, dalilain da ya sa gwamnati ta dage kusan dukkan tsauraran matakan da ta gindaya. 

Kamar yadda shugaba Cyril Ramophosa ya sanar, an sauke matakan kullen daga mataki na uku zuwa daya. Mahukuntan kasar sun dage dokar hana fitar dare, kuma za a iya yin taron mutanen da yawansu ya kai 250 a waje, kana mutum dari za su iya haduwa a cikin babban daki.

Bayyanar sabon nau'in cutar ta corona dai ya kawo fargaba a kasar da a baya akan samu a kalla mutane dubu 20 sabbin kamuwa, sannu a hankali ya dawo dubu hudu, inda cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta sanar da cewar, sabbin kamuwa basu shige 1,200 ba cikin tsukin mako guda. Ana danganta nasarar da yanayi na zafi da aka fara a Afirka ta Kudu. Sai dai har yanzu wajibi ne a saka takunkumi.

Kisan al'umma a yankin Tigray na Ethiopiya

Sudan Grenze Äthiopien | Tigray | Um Rakuba-Flüchtlingslager Essensausgabe
'Yan Tigray na layin karbar abinciHoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

A labarinta mai taken " Su na kashe mu kowa yayi shiru" Jaridar Die Zeit ta ce yanzu haka yunwa na barazana a yankin Tigray mai kwarya kwaryar 'yancin kai.

Amanuel Tesfay ya dauki tsawon lokaci yana rokan Allah fita daga wannan yanayi da ya tsinci kanshi a ciki. Yana fatan samun layin waya da zai bashi damar magana da mai dakinsa Fereweyni da 'ya'yanshi uku da rikici ya raba su.

Mai shekaru 35 da haihuwar kuma mai abun rufin asiri daga kasuwancin ridi, Tesfay ya kasa fahintar yadda ya tsinci kanshi a matsayin dan gudun hijira a kauyen Hamdajet da ke kan iyakar Ethiopiya da Sudan.

Ya kasance daya daga cikin matasan da yakin wannan kasa ta kahon Afirka mai fada aji, mai yawan al'umma miliyan 110 ya ritsa da su. Rikicin dai ya haifar da barazanar yunwa tsakanin al'umma, ba wai a kasar kadai ba amma ya na iya kasancewa babbar barazana har ga Turai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani