1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus 24.05.2024

Usman Shehu Usman ZUD
May 24, 2024

Yunkurin juyin mulkin da ya faru a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na ci gaba da daukar hankali a ciki da wajen kasar.

https://p.dw.com/p/4gEry
Shugaban Kwango Félix Tshisekedi
Hoto: DW

Jaridar Frankfurter Algermeine Zeitung ta ce yunkurin juyin mulkin ya haifar da tambayoyi da yawa game da abubuwan da suka faru a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Ta ci gaba da cewa wani dan Kwango mazauni a Amurka dauke da makamai ya kama hanyarsa ta kutse zuwa fadar gwamnatin kasar da ke a Kinshasa, babban birnin kasar ta Kwango.

Shugaban Kwango Félix Tshisekedi
Hoto: DW

A cikin faifan bidiyon kai tsaye a Facebook, ana iya ganin masu dauke da makaman a kofar shiga ginin da ke ofishin shugaban kasa. Wasu suna daga tutar kasar wato Zaire mai launin haske, sunan da ake kiran kasar daga 1971 zuwa 1997. Suna son 'yantar da Kwango, in ji jagoransu. "Za mu farka a cikin kasar da ta fi kyau fiye da da. "Félix ya tafi." Wannan yana nufin Shugaba Félix Tshisekedi. Daga bisa gwamnati ta ce yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Félix Tshisekedi ne da bai yi nasara ba.

Yakin basasar Sudan

Jaridar die Tageszeitung ita kuwa ta duba yakin basasa a Sudan, inda ta ruwaito cewa wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin kisan gillar da aka yi a yankin Darfur, Gaza da kasar Kwango da Sudan ya kasance babbar masifa. Yawan fararen hula da ke fama da irin wannan rikici, shi ne kusan ya dauki hankalin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Wakiliyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan kisan kare dangi ta bayyana bacin ransa  da abin da ke faruwa a yankin Darfur, inda ya fada wa kwamitin sulhun cewa "halin da ake ciki yanzu yana nuna kowace alamar hadarin kisan kiyashi kuma ana zargin cewa an riga an aikata wannan laifi".

Yadda yaki ya tagayyara yankin Darfur na Sudan
Hoto: Albert Gonzalez Faran/Unamid/Han/dpa/picture alliance

Wakiliyar ta musamman mai kula da rigakafin kisan kiyashi, Alice Wairimu Nderitu, ta yi gargadin ne ga Majalisar Dinkin Duniya a a farkon wannan mako. Taron dai wani taro ne na musamman na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka bude wa dukkan kasashe mambobin MDD bisa kare fararen hula a fadace-fadacen da ke dauke da makamai, tare da rahoton shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya a matsayin babban misali. Rahoton na bana ya ce an samu karuwar kashe fararen hula da kashi 72 cikin darin idan an kwatanta da bara.

Zaben Afirka ta Kudu na 2024

Jaridar Süddeutscher Zeitung ta yi sharhinta kan siyasar Afirka ta kudu, tana mai cewa ba a yarda Jacob Zuma ya tsaya takara ba domin an yanke wa tsohon shugaban na Afirka ta Kudu hukunci a shekarar 2021, bisa hakan ne aka haramta masa shiga zaben.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Hoto: AP/picture alliance

Kwanaki tara gabanin zaben Afirka ta Kudu, kotun kolin kasar ta sanar da wani mataki mai muhimmanci a farkon makonn nan. Ba a yarda tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya tsaya takarar majalisar dokokin kasar ba. Kotun ta ce an yanke wa Zuma hukuncin daurin fiye da watanni goma sha biyu a shekara ta 2021 - shekaru uku bayan ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kasa. A Afirka ta Kudu, irin wannan hukunci yana daidai da dakatar da rike mukaman gwamnati na tsawon shekaru biyar. A baya shi kansa da kuma sabuwar jam'iyyarsa ta MK sun yi nasara a jimillar kararraki uku da ka iya hana su shiga zaben, inda a kotun baya ta ce Zuma zai iya tsayawa takara. Yanzu dai kotun kolin ta soke wannan hukunci.

Halin da ake ciki a Maroko

Jaridar Neue Zürscherzeitung ta ce shirin garambawul ya raba kan kasar Maroko, inda misali masu kishin Islama suna adawa da soke auren mata fiye da daya. A shekaru 25 da suka gabata, Sarki Mohammed na shida ya hau mulkin kasar Maroko da nufin sabunta tsarin dokokin mulkin kasarsa. Sai dai babban burinsa na kawo sauyi, wato sauya dokokin iyali na gargajiya da daidaito tsakanin maza da mata, na zama wani aiki mai wahala a gare shi.