1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
November 13, 2020

Zaben kasar Cote d'Ivoire da rikicin kasar Habasha da kuma batun cin hanci da rashawa a Afirka ta Kudu sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3lGNN
Elfenbeinküste Abidjan | Wahlen | Präsident Alassane Ouattara
Shugaba Alassane Ouattara ya yi tazarce a wa'adin mulki karo na uku Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Jaridar Die Tageszeitung ta rubuta labarinta ne game da halin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire, bayan zaben kasar da ya bai wa shugaba Alassane Ouattara damar zarcewa a karo na uku. Jaridar ta ce, tun bayan sanar da sake zabar shugaba Ouattara ne dai aka san cewar akwai sauran tsalle a wannan kasa ta yammacin Afirka. A unguwar Yopougon mafi yawan al'umma a birnin Abidjan kuma daya daga cikin yankunan da madugun adawar kasar ke da magoya baya, mutane na ci gaba da labewa a gidajensu. Kafin makonni biyu da suka gabata dai lamura na tafiya daidai, kana mutane na tafiyar da harkokinsu na yau da kullum. Kwatsam sai komai ya sauya tun bayan da aka sanar da sakamakon zaben kasar mai sarkakakiya.

Tarhi 

Yanzu haka dai duk tafiyar mitoci 50 akwai shingen bincike a kan hanya kuma dole mutum ya tsaya. Akwai matasa da ke zaune a gefen hanya suna lura da duk wata bakuwar fuska da ta shigo wannan yankin. Tamkar dai shekara ta 2010 bayan zaben shugaban kasa, lokacin da tsohon shugaba Laurent Gbagbo wanda shi ne kan kujerar mulki a wancan lokaci, ya ki amincewa da shan kaye, inda ya yi watsi da nasarar da shugaba mai ci a yanzun Alassane Ouattara ya samu. Rikicin da ya yi sanadiyyar rayukaun sama da mutane 3,000.
Wani batu da ya fi daukar hankalin duniya a yanzu haka shi ne fargabar halin da kasar Habasha ta tsinci kanta a ciki, iniji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ci gaba da cewar mako guda bayan kazamin fada a yankin Tigray da ke arewacin kasar, Firaminista Abiy Ahmed na da yakinin cewar komai ya kusan zuwa karshe. Gwamnatin Adis Ababa dai ta sanar da kwato wani muhimmin filin saukar jiragen sama da ke birnin Humera daga wajen mayakan fafutukar kwato 'yancin Tigray da ake kira TPLF a takaice. Sai dai acewar sharihin jaridar ko shakka babu, rikicin da ya barke tsakanin gwamnati da masu fafutukar na Tigray na kara kazanta.

Äthiopien | Addis Abeba | Unruhen in der Tigray-Provinz
Rikicin Habasha ya tilastawa mutane musamman mata da kananan yara gudun hijiraHoto: picture alliance/AP Photo

Fargabar shiga halin tasku

Kawo yanzu dai an ruwaito mutuwar mutane masu yawa baya ga wadanda suka jikkata kuma suke jinya a asibiti. Haka kuma wasu dubbai sun tsere zuwa kasar Sudan da ke makwabtaka. Akwai rahotannin hare-hare ta sararin samaniya. Masu lura da lamura da ka je su zo na nuna damuwa dangane da halin da fararen hula ke ciki, ban da illar da wannan rikici zai yiwa kasar idan har ba a shawo kansa cikin lokaci ba. Habasha dai na zama kasa ta biyu mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, kuma daya daga cikin kasashen da suka fi karfin soja a wannan yanki na Kahon Afirka. Ana dai kuma ganin rikicin, zai iya shafar kasashen dake makwabtaka ta ita, tare da tayar da zaune tsaye a yankin baki daya.
Daga batun rikici sai kuma na yaki da rashawa a kasar Afirka ta kudu. A labarinta mai taken, "cafke babban sakataren jam'iyyar ANC na zama kololuwar yaki da rashawa na shugaba Cyril Ramaphosa cikin jam'iyyarsa," jaridar Die Tageszeitung ta ce a ranar 10 ga watan Nuwamban da muke ciki yawancin gidajen talabijin da radiyo suka tsayar da yada shirye-shiryensu: An kama babban sakataren ANC Ace Magashule!

Südafrika Präsident Ramaphosa
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta KuduHoto: AFP

Matakin ba-sani-ba-sabo

Hukumar kolin kasar da ke yaki da rashawa ta tabbatar da cafke mutum na biyu mafi karfi a jam'iyyar da ke mulki, bayan da shugaban kasar ya shaidawa alkali zarginshi da ake yi na sama da fadi da miliyoyin kudi, kuma 'yan sanda za su kamo shi idan yaki gurfana. Ana zargin sa da sama da fadi da wajen Euro miliyan 14 a karskashin shirin samar da gidaje na gwamnati a 2014. Cikin makonnin da suka gabata dai, an cafke manyan 'yan jam'iyyar da ke mulki da 'yan kasuwa 13. Yaki da cin hanci da rashawa na cikin alkawuran da shugaba Cyril Ramaposa ya dauka lokacin da ya sha rantsuwar kama mulki a watan Fabarairun 2018.