Afirka a 2018: Fata na gari lamiri
Zaman lafiya tsakanin Habasha da Iritiriya, rikici a Kamaru da Kwango, ta'addanci a Mozambik da Mali, yaki da cin hanci a Angola da Afirka ta Kudu. Shekara ta 2018 a Afirka. Waiwaye a cikin hotuna.
Sulhu a kasar Kenya
A watan Maris shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da madugun 'yan adawa Raila Odinga sun yi masafaha. Bayan zargin yin magudin zabe, an sake gudanar da zaben 2017. Odinga ya kaurace wa zaben zagaye na biyu kana ya bari aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa na al'umma.
Yaki da cin hanci da rashawa da rashin daidaito a Afirka ta Kudu, Zuma ya yi murabus
A farkon shekarar Shugaba Jacob Zuma ya mika wuya ga matsin lambar ANC, ya yi murabus bayan shekaru tara kan mulki. Yana fuskantar shari'a gaban kotu dangane da cin hanci da halatta kudin haramun da zamba. Magajinsa Cyril Ramaphosa ya kaddamar da sauye-sauye na mallakar filaye don yaki da rashin daidaito a kasar.
Matsin lamba kan kungiyoyin farar hula a Tanzaniya
Shugaba Magufuli na tafiyar da mulkin kama karya. An takaita ayyukan kungiyoyin farar hula, ba a yarda mata 'yan makaranta da suka yi ciki su tafi makaranta ba, ana cin zarafin 'ya luwadi da madigo. A karshen shekara kungiyoyin kasa da kasa da yawa sun rage yawan taimakon raya kasa don matsa wa shugaban lamba ya sassauto.
Zaman lafiya tsakanin Habasha da Iritiriya bayan shekaru 20
"Tsuntsun zaman lafiya" lakabin da kamfanin Ethiopian Airlines ya yi wa jirgin saman da ya tashi daga Addis Ababa zuwa Asmara ke nan a watan Yuli, shi ne na farko ya tashi kai tsaye daga Habasha da Iritriya da suka kwashe shekaru gommai suna gaba da juna. Iyalai da aka raba shekaru da dama sun sake rungumar juna, sakamakon shirin zaman lafiya da sabon Firaministan Habasha ya kaddamar.
Yaki da cin hanci a kasar Angola
Shugaban kasar Angola João Lourenço ya kama aiki don kawo karshen yawan nuna son kai a kasar. A 2018 shi ma José Filomeno dos Santos (a hoto) da ake wa lakabi da Zenu, ya ji shi a jika. Dan tsohon shugaban kasa José Eduardo dos Santos, an kai shi gidan wakafi saboda zargin cin hanci. A dole 'yar uwarsa ta sauka daga mukamin shugabar kamfanin mai na kasa a 2017.
Joseph Kabila ba zai tsaya takara ba
Bayan kai komo na dogon lokaci, Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwango ya sanar cewa ba zai sake stayawa takara a zaben watan Disamba ba. Ya nada tsohon ministan cikin gida Emmanuel Ramazani Shadary a matsayin wanda zai gaje shi. An hana 'yan takarar nan masu angizo wato Jean-Pierre Bemba da Moïse Katumbi tsayawa takara. Kan 'yan adawa ya rarrabu.
A watan Nuwamba sojojin Jamus sun karbi jagorancin tawagar horas da sojoji a Mali
Har yanzu babu tabbas kan yanayin tsaro a Mali duk da kasancewar dakarun ketare. Saboda barazana daga masu kaifin kishin addini daruruwan tashoshin zabe daga cikin dubu 23 sun kasance a rufe a lokacin zaben shugaban kasa na watan Agusta. Bayan wasu korafe-korafe na 'yan adawa a karshe an sake rantsar da shugaban kasa mai ci Ibrahim Boubacar Keïta.
Kyautar zaman lafiya ta Nobel ta 2018 ga mai fafatukar kare hakin dan Adam Nadia Murad da likitan Kwango Denis Mukwege
Dukkansu biyu sun sadaukar da ransu wajen yaki da masu amfani da cin zarafi a matsayin makami a lokacin yaki. Likitan mata Mukwege yana yi wa matan da aka ci zarafinsu ko aka yi musu fyade, jinya a asibitin da ya gina da ke a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.
Makarantu sun kasance a rufe a yankin masu magana da Ingilishi na Kamaru
Alkalumman da kungiyar Amnesty ta bayar sun nuna cewa fararen hula 400 suka rasu a rikici tsakanin gwamnati da 'yan aware. Ana yawaita rufe makarantu, sanan a lokacin zaben watan Oktoba an rufe tashoshin zabe da yawa. Kashi 53 cikin 100 na 'yan Kamaru suka kada kuri'a a zaben, inda aka sake zaban Shugaba Paul Biya a sabon wa'adi na mulki na shekaru takwas.
Jerin hare-hare sun addabi lardin Cabo Delgado da ke arewacin Mozambik
Wasu da ba a gane su ba sun farma ofisoshin 'yan sanda, sun cuna wa motoci da gidaje wuta, sun yi harbi na kan mai uwa da wabi da bindigogi masu sarrafa kansu, kana sun daddatsa mutane da adduna. Akasari wadannan maharan Musulmi ne, sai dai ba a gano alakarsu da kungiyar IS ba. A cikin watan Oktoba na kame mutane fiye da 200 da ake zargi da ta'addanci.
"Compact with Afrika" - Waiwaye na cikakken hadin kai
A taron kolin na birnin Berlin wato "Compact with Africa" da ya gudana cikin watan Oktoba, an yi waiwaye bayan shekara daya da rabi. Yawan kamfanonin Jamus da ke saka hannun jari a Afirka na karuwa sannu a hankali. Shugabar gwamnati Angela Merkel a nan a tsakanin shugaban Ruwanda Paul Kagame da na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, sun sanar da kafa sabon asusu na Euro miliyan dubu daya.