1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Dusar kankara ta hallaka mutane 25

Abdullahi Tanko Bala
February 19, 2024

Dusar kankara ta hallaka mutane 25 a gabashin Afghanistan

https://p.dw.com/p/4cabr
Zubar dusar kankara a Afghanistan
Hoto: ABDUL BASIT/AFP

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da zubar dusar kankara sun janyo zaizayar kasa a gundumar Nuristan a gabashin Afghanistan wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 25 yayin da wasu da dama kuma suka makale a cikin baraguzai

Ana ci gaba da aikin ceto inda ake kyautata tsammanin yawan wadanda suka rasu na iya karuwa.

Aghanistan ta saba da tsananin sanyi sai dai a bana an sami jinkiri fara zubar dusar kankarar.