Adly Mansour ya yi jawabin bankwana | Labarai | DW | 04.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adly Mansour ya yi jawabin bankwana

Shugaban rikon kwarya na Masar Adly Mansour ya yi jawabin bankwana ga al'ummar kasar inda ya shawarcesu da su tsaya tsayin daka wajen kare kimar kasarsu a idon duniya.

Shugaban rikon kwarya na Masar Adly Mansour ya shawarci al'ummar kasar su tashi haikan wajen kawar da kalubalen da kasar ke fuskanta wanda suka hada da tabarbarewar tsaro da koma bayan tattalin arziki gami da rudani na siyasa.

Mr. Mansour ya yi wannan kiran ne a wani jawabin bankwana da yi mai sosa rai matuka, inda ya ke cewar dole Misrawa su tsaya tsayin daka wajen kare kimar kasarsu a idanun duniya.

Adly Masour dai wanda a baya shi ne shugaban kotun kolin kasar ya shafe kusan shekara guda kan wannan matsayi na shugaban rikon kwarya kuma nan gaba zai mika ragamar jagorancin Masar din ga Abdul Fatah al-Sisi wanda ya samu gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a kwanakin da suka gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal