ADC na shirirn lashe zaben Lesotho | Labarai | DW | 02.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ADC na shirirn lashe zaben Lesotho

Jam'iyyar Firaminstan kasar Lesotho Thomas Thabane ta ADC ce ke kan gaba a zaben 'yan majalisun dokokin kasar da aka gudanar.

Jam'iyyar ta ADC dai ta lashe zaben a yankuna 38 cikin 60 din da aka kammala kidaya kuri'un da aka kada. An dai gudanar da zaben ne a ranara Asabar din da ta gabata shekaru biyu gabanin lokacin da ya kamata a gudanar da shi domin dawo da doka da oda a kasar da ke yankin kudancin Afirka watanni shida bayan da aka zargi sojojin kasar da yunkurin juyin mulki. Jam'iyyar adawa ta DC karkashin jagorancin tsohon Firamminstan kasar Pakalitha Mosisili ce ke a matsayi na biyu bayan da ta lashe zaben a yankuna 20 na kasar yayin da jam'iyyar LCD karkashin jagorancin mataimakin Firaminstan na Lesotho ke mara mata baya a matsayin ta uku.