Duniya na nuna adawa da wariyar launin fata
June 7, 2020Duk da matsalar annobar corona da kasashen duniya ke fama da ita, dubun-dubatar jama'a sun fito yin zanga-zanga a wasu sassa dabam-dabam na duniya a ciki har da nan Jamus, da nufin nuna rashin jin dadin kan wariyar launin fata da takurawar 'yan sanda a wasu kasashen duniya, biyo bayan mutuwar da Goerge Floyd ya yi a hannun wani dan sanda a kasar Amirka.
Wata majiyar 'yan sanda a tarayyar Jamus ta sheda cewa akalla mutun fiye da 25. 000 ne suka fito yin zanga-zangar a birnin Munich kawai, a yayin da wasu da dama suka fito yin boren a Berlin da Hambourg da birinin Kolon.
A kasar Amirka inda zanga-zangar ta samo asali sakamakon kisan George Floyd, an gudanar da zanga-zanga mafi girma a wasu jihohi kamar su Philadelphie da New York da birnin Washington D.C, inda rahotanni suka ce a Washington an dauki kwakwaran matakan tsaro na killace fadar gwamnatin Amirka.