Adawa da gwamnatin Banizuwela | Labarai | DW | 03.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adawa da gwamnatin Banizuwela

Ana ci gaba da zanga-zangar adawa da shirin Shugaba Nicolas Maduro na Banizuwela na sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaba Nicolas Maduro na Banizuwela ya gamu da cikas bisa shirin samar da sabon kundin tsarin mulki. 'Yan adawa da ke da rinjaye a majalisar dokoki sun nuna rashin goyon baya ga shirin shugaban na samar da sabon kundin tsarin mulki.

'Yan adawa na cewa Banizuwela ba ta bukatar sabon kundin tsarin mulki, sai dai sabon shugaban kasa, kana majalisar za ta katse hanzarin samar da wani sabon kundin tsarin mulkin. Tuni dai dubban masu zanga-zanga a birnin Caracas fadar gwamnatin kasar ta Banizuwela da ke yankin Latin Amirka ke ci gaba da gangamin nuna rashin goyon baya ga shugaban.