Adama Barrow na shirin rantsuwar kama aiki | Labarai | DW | 19.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adama Barrow na shirin rantsuwar kama aiki

Ana shirin rantsar da zababben shugaban Gambiya Adama Barrow a kasar Senegal yayin da a waje guda kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a domin amfani da karfin soji wajen tumbuke Jammeh.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirin kada kuri'a kan kudirin da zai ba ECOWAS damar turawa da sojoji don tumbuke shugaban kasar Gambiya daga kan mulkin kasar wanda wa'adin mulkin sa ya cika. 

A daidai lokacin da zababben shugaban kasar Gambiya Adama Borrow ke kasar Sinegal don rantsar da shi a matsayin shugaban kasar ta Gambya a ofishin Jakadancin Gambiya da ke Senegal.


Wata jami'a daga cikin masu sasanta tsakani kan rikici na Gambiya Isatou Touray ta bayyana cewa ya zuwa yanzu,ba a sanar da su lokaci da kuma wurin da za a rantsar da zababben shugaban kasar ba, sai dai ta ce tana da tabbacin za a rantsar da shi a ofishin jakadancin Gambiya da ke kasar ta Senegal.

Yayin da ta yi maraba da tsokacin da shugaban rundunar sojin kasar Ousman Badjie ya yi cewa sojin kasar ba za su hana tumbuke Yahya jemmeh daga shugabancin kasar ba.