1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Abu Namu: Wasu mutanen da ake kira mata-maza.

Ramatu Garba Baba AAI
February 24, 2020

Ana samun wasu mutanen da ake kira mata-maza wadanda ake haifarsu da al'aurar maza da kuma ta mata. Inda a wasu kasashen Afrika, iyayen da suka haifi mata-maza kan dauka cewa an yi musu baki ne, don haka su kan kalli lamarin a matsayin abin kunya ko ma abin neman tsari.

https://p.dw.com/p/3YLHt

A shirin na Abu Namu ya yi nazari ne kan wasu mutane da ake kira mata-maza wadanda ake haifarsu da al'aurar maza da kuma ta mata. Inda a wasu kasashen Afrika, iyayen da suka haifi mata-maza kan dauka cewa an yi musu baki ne, don haka su kan kalli lamarin a matsayin abin kunya ko ma abin neman tsari. Kamar yadda masana ke fadi akwai bayani a kimiyyance game da yadda halittar mata-maza ke kasancewa. Camfi da tsangwama da matsin tattalin arziki ga wadanda suka nemi gyara halitta na daga cikin dimbin matsalolin da mata-maza ke cin karo da su a rayuwa. To sai dai wannan shirin zai mayar da hankali ne ga bangaren al'umma kamar yadda za a saurara.