1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu na Mu: Hotuna kafin aure

Ramatu Garba Baba YB
December 26, 2018

Wasu dai na ganin hotunan sun saba wa addini da al'adar Malam Bahaushe yayin da wasu ke ganin ai wayewa ce da zamani gara a gwangwaje.

https://p.dw.com/p/3Ab0n
Africa Child Marriage Mosambik
Hoto: picture alliance/AP Photo/S.Mohamed

A shirin na wannan lokacin ya mayar da hankali kan batun hotunan gabanin bikin aure da aka fi sani da "Pre Wedding Photos." Amarya da ango na daukar hotunan kala daban daban dauke da labarin zuci, inda suke sanya tufafi tare da caba ado tamkar ranar bikin auren, a wasu lokuta ma akan hada ire-iren wadannan hotuna da waka da aka tsara don masoyan kafin a sake su a shafuka na sada zumunta na zamani.

A yayin da wannan yayin ke daukar hankulan jama'a, wani abu da ya sha banban shi ne sabanin ra'ayi da ake samu akan ire-iren hotunan da muke magana a kansu, wasu na ganin abin birgewa ne da ke kuma nuna tsantsar soyayyar da ke tsakanin angon da amaryar wasu kuwa na ganin ya saba wa alkunya irin na al'adar malam Bahaushe a wasu lokuta ma ana ganin abu ne da ya saba wa addini, mun nemi ji daga bakin wasu daga cikin jama'ar gari musanman matasa don jin ra'ayoyinsu. Ana iya latsa shirin mai dauke da sauti a kasa don jin cikakken shirin.