1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abincin da mai ciwo suga ya kamata ya ci

Abdourahamane Hassane
March 22, 2019

Masana kiwon lafiya sun bada shawara kan nau'in abinci da mai ciwon suga ya kamata ya ci domin kiyaye lafiyarsa da kuma kare kansa daa kamuwa da wasu cutattuka.

https://p.dw.com/p/3FWt4
Ballaststoffe
Hoto: Colourbox

Akwai abinci iri iri da ake bukatar mai ciwon suga ya rika ci don kasancewa cikin koshin lafyarsa. Ana so mai ciwon suga ya kauracewa shan suga da dangin duk wasu kayan zaki da kaiya janyo masa hawan suga.

Likitoci sun yi gargadin cewar wanda ke fama da ciwon  suga ba zai rika cin kayan marmai irin su Inibi da Abarba ba, yayin da wasu  nau’in kayan marmari kamar su Mangwaro da Ayaba sai dai a sha kadan.

Sannan ya kamata a rika yin awon jini yi a kai a kai daga b lokaci zuwa lokaci domin ganin tsirin abinci da ake ci ko sugan na sauka ko kuma yana karuwa.