Abidjan: Hatsarin jirgin sama ya hallaka mutane | Labarai | DW | 14.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abidjan: Hatsarin jirgin sama ya hallaka mutane

Wani jirgin sama daukar kaya na kasar Ukraine dauke da mutane 10 da suka hada da 'yan kasar Faransa hudu da 'yan Maldoviya shida ya fadi a cikin teku a birnin Abijan na Cote d'Ivoir

'Yan kasashen Maldoviya da Faransa  guda takwas ne suka mutu, kana wasu 'yan Maldoviyan guda biyu suka samu raunuka, inda ake kula da su a asibin sojojin Faransa da ke kusa da filin jirgin saman na Abidjan.

Babban jirgin na daukan kaya na kasar Ukraine, jirgi ne da sojoji ke amfani da shi wajen daukar kayayakinsu, kuma a wannan karo sojojin Faransa ne suka yi hayarsa. Sojojin kasar ta Faransa da ke birnin Abidja na kasar Cote d'Ivoir na aiki ne kafada da kafada da rundunar sojojin na Faransa a yankin Sahel ta Barkhane da ke da cibiya a birnin NDjamena na kasar Chadi.

Sai dai kuma wata majiyar na cewa jirgin ya tashi ne daga birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso zuwa filin jirgin sama na birnin Abidjan, kafin ya fadi a cikin teku yayin da yake kokarin sauka.