Abdel Fattah al-Sissi ya samu nasara a zaɓen Masar | Siyasa | DW | 28.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Abdel Fattah al-Sissi ya samu nasara a zaɓen Masar

Sakamakon farko na zaɓen da hukumar zaɓen ƙasar Masar ta Bayyana na nuna cewar Al Sissi shi ne ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala wanda kafofin watsa labarai na ƙasar suka yaɗa batun.

Kwamitocin yaƙin zaben na 'yan takarar biyu dai,sun nuna rashin jin daɗinsu dangane da yadda masu zaɓen ba su fito ba da kuma ƙarin wa'adin da hukumar ta yi. Magoya bayan Alsisi dai na ɗaukar cewar ,ƙarin zai sa mutane su tabbatar da zargin rashin fitar mutane da ake ta yi,a yayin da su kuma magoya bayan Sabbahi,ke cewar,ga dukkan alamu,akwai lauje cikin naɗin. Hukumar zaɓen dai ta ce babu gudu ba ja da baya kan wannan ƙarin da zai bai wa waɗanda tsananin zafin da ake yi a ƙasar ya hanasu fita.

Rashin jin dadin gwamnatin dangane da rashin fitar jama'a a zaɓen

Gwamnatin wuccin gadi,da ta ba da umarnin bai wa duk wanda ke nesa da mazaɓarsa tikitin komawa gida kyauta don ya kaɗa ƙuri'arsa,ta ƙara da yin gargaɗi na ci tarra ga waɗanda ba su halarci zaɓen ba, abin da ya janyo maratanin jama'a kamar yadda wani msanin kuɗin tsarin mulki ya bayyana.

"Cin tarra kan wanda bai yi zaɓen ba,zai mayar da zaɓen ya zama kamar wani aikin dole ba , a gaskiyya yadda lamarin yake,zaɓe hakki ne da ganin dama ba wajibi ba kan yan ƙasa."

Daga ƙasa ya a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi: Mahmud Azare Yaya
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin