Abbas ya gamsu da ganawar da ya yi da Ehud Olmert
August 7, 2007Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya bayyana gamsuwa da tanttanawar da yayi da Praministan Isra´ila Mahmud Abbas, wadda ta gudana yammacin jiya, a birnin Jericho, na gaɓar yamma ga kogin Jordan.
Abbas ya bayyana hakan, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga Palestinawa, a game da sakamakon da taron ya cimma.
A cewar sa, wannan shine karon farko, da ɓangarorin 2 su ka cimma matsaya ɗaya a game da batutuwa masu mahimmanci.
Tun mako mai zuwa Isra´ila ta alƙawarta cire wasu shingaye da ta gitta, domin baiwa Palestinawa damar gudanar da zirga-zirga.
To saidai har yanzu, taron bai bayyana kamai ba, a game da batun iyakokin ƙasar Palestinu.
Saidai a ta bakin tsofan Praminista Isma´il Haniey, wanda ƙungiyar sa ta Hamas ke riƙe da zikin Gaza,taron na jiya ba yi nasara ba.
Mahalarta taron Jericho, sun tafi da burin masanyar ra´ayoyi, a game da wannan batu mai sarƙƙaƙiya, da zumar cimma matsaya guda, kamin watan november mai zuwa, wanda a cikin sa ne, Amurika ke sa ran kiran wani taron ƙasa da ƙasa, domin tanttana batun girka ƙasashe 2 na Isra´ila da Palestinu masu maƙwataka da juna cikin girma da arziki.