A zabi sabon shugaban kasar Iceland | Labarai | DW | 26.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A zabi sabon shugaban kasar Iceland

An zabi Gudni Johannesson a matsayin sabon shugaban kasar Iceland bayan kirga galibin kuri'un da aka kada a wannan Asabar da ta gabata.

Gudni Johannesson ya lashe zaben shugaban kasar Iceland wanda ya gudana a wannan Asabar da ta gabata bayan samun kashi 38 da doriya cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da shamhakiyar 'yar kasuwa Hallan Tomasdottir ta mara masa baya da kashi 29 cikin 100. Johannesson ya bayyana lashe zaben bayan kirga galibin kuri'un da aka kada.

Zababben shugaban kasar ta Iceland Johannesson dan shekaru 48 da haihuwa ya shafe tsawon rayuwarsa yana sharhi kan lamaran yau da kullum, kana babban malamin jami'a.

Bisa tsarin zaben kasar dan takara yana bukatar samu kuri'a mafi rinjaye ne kawai, domin haka Gudni Johannesson zai dauki madafun iko ranar daya ga watan Agusta mai zuwa ba tare da zuwa zagaye na biyu na zabe ba, inda yake da wa'adin shekaru hudu kafin sake zabe.