A wannan Alhamis din ce ake hawan Arfa
October 25, 2012Talla
Tun a jiya Laraba ce dai maniyata aikin hajjin na bana sanye da harami su ka fara fita zuwa Muna inda za su share akasarin yau su na gudanar da ibada a filin na Arfa wanda shi ne kololuwa na aikin hajji.
Hukumomin Saudiyya dai sun ce kimanin mutane miliyan biyu da rabi ne za su gudanar da aikin hajjin na bana wanda miliyan daya da dubu dari bakwai su ka fito daga ƙasashen duniya daban-daban.
Saudiyyan dai ta ce ta yi kyakkyawan shiri da nufin bawa mahajjata damar yin aikin cikin kwanciyar hankali da kuma yanyi na tsafta da kyakkyawan tsaro gami da ɗaukar matakai na kula da lafiyar mahajjatan.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu