A Tuniziya matasa na koyi da mutumen nan da ya bankadawa kansa wuta | Labarai | DW | 25.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Tuniziya matasa na koyi da mutumen nan da ya bankadawa kansa wuta

Tun bayan da Tuniziya ta rungumi juyin juya hali,matasan kasar na kokawa bisa ga rashin aikin yi,inda suke cewa gwamma jiya da yau.

default

Matasa na fuskantar rashin aikin yi a Tuniziya

Rahotani daga Tunis baban birnin Tuniziya,sun tabbatar da mutuwar wani matashi dan shekaru 17 da haifuwa bayan da ya rungunmi karfen tagarahon wutar lantarki a garin Buzid inda nan ne ke matsayin cibiyar zanga zanagar da ta yi sandiyar kifar da gwamnatin shugaba Zin Al-Bedine Ben Ali a shekara ta 2011.
Shi dai Wissem Hani matashi ne da ke daya daga cikin dubban matasasa a kasar da ke nuna bacin ransu a dangane da matsalar aikin yi bayan kammala karatun. Garin da ya yi suna tun bayan da Mohamed Buwazizi ya kunnawa kansa wuta domin nuna rashin amuncewarsa da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na galazawa masu kananan sana'o'i.
To dama dai a yayin bukukuwan cikon shekaru 2 da soma juyin juya halin,matsan garin sun ce muddun hukumomin kasasr ba su kawo sauyi ba,to babu shakka kowa ma na iya zama Mohamed Buwazizi matashin da ya bankadawa kansa wuta.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Saleh Umar Saleh