A Tunisiya an harbe wani dan adawa | Labarai | DW | 25.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Tunisiya an harbe wani dan adawa

Dubban jama'a sun shiga zanga-zanga bayan bindige wani fitaccen dan adawan Tunisiya

Radical Islamist movement Ansar al-Shariah supporters clash with Tunisian police officers after Tunisia's Interior Ministry on Friday banned their annual conference supposed to be held in Kairouan, in Ettadhamen, near Tunis, Sunday May 19, 2013. Massive numbers of Tunisian police and army surrounded Tunisia's religious center of Kairouan to prevent a conference by a radical Islamist movement that has been implicated in attacks around the country. (AP Photo/Nawfel)

Masu zanga-zanga a Tunisiya

Wani labari da ya fito daga kasar Tunisiya na cewa an harbe wani ƙosa a jam'iyar adawan ƙasar kasar. Labarin wanda wani gidan radio a yankin da aka yi harbin ya fara fitarwa, yace an harbe Mohamed Brahmi har lahira a Tunis babban birnin ƙasar Tunisiya. Watanni shida da suka gabata ne dai, aka harbe wani fitaccen dan adawa Chokri Belaid, abinda ya yi sanadiyar barkewar zanga-zanga a fadin ƙasar. Kasar Tunisiya dai har yanzu ba ta samu kammala inganta matakan tsaro ba, tun bayan juyin juya hali, wanda ya kifar da gwamnatin a bisa boren talakawa.

Mawallaf: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasir Awal