A ranar larabar nan ce ake rantsar da Firiministan kasar Canada. | Labarai | DW | 04.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A ranar larabar nan ce ake rantsar da Firiministan kasar Canada.

Canada na shirye-shiryen rantsar da sabon Firiministan kasar Justin Trudeau dake kasancewa Firiminista na 23 a dai- dai lokacin da ya bayyana raba daidai na yawan mukaman majalisar a tsakanin maza da mata.

Trudeau dai shine da na farko ga wani Firiministan kasar da ya karbi madafun ikon kasar kana kuma mafi kankantar shekaru da ya kai ga darewa kujerar firaministan kasar da shekaru 43 a duniya, na cigaba da janyo hankulan al'ummomin kasa da kasa a bisa karancin shekarun sa a fagen siyasa.

Kazalika bikin rantsar dashi zai kawo karshen shekara da shekarun da 'yan ra'ayin rikau a karkashin jagorancin Firiminista Stephen Harper wanda yanzu jam'iyyar sa ta zama yar hamayya.

Sabon Friministan dai yayi alkawarin sake bude wani sabon babi ga huddar dangantakar kasashe gami da raba daidai a tsakanin mata da maza a sabuwar majalisar sa.