1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Najeriya an bankaɗo satar dukiyar ƙasa

Usman ShehuNovember 20, 2012

Wani kwamitin bincike ya gano ya mummunar satar kuɗin gwamnati da ma'aikatu ke yi

https://p.dw.com/p/16mxj
LAGOS, NIGERIA - JULY 15: A detail of some Nigerian Naira,(NGN) being counted in an exchange office on July 15, 2008 in Lagos, Nigeria. (Photo by Dan Kitwood/Getty Images)
Wani ke ƙirga damin nairoriHoto: Getty Images

A lamarin da ke kara nuna yadda matsalar cin hanci da rashwa da ma karkatar da dukiyar al'umma ke kara yin kamari a Najeriya, gwamnati ta sake asarar Naira triliyan 4 a tsakanin ma'aikatun gwamnatin kasar, abinda kwarraru ke nuna damuwar hatsarin da ke tattare da hakan.

Wannnan sabon bayanin da ke nuna yadda ma'aikatun gwamnatin Najeriyar ke karkatar da dukiyar gwamnatin kasar da ke kunshe a cikin wani sabon rahoto, wanda babban mai binciken kudi na Najeriyar ya fitar a kan yadda aka kashe kudadden gwamnati a kasar, abinda ya nuna irin yadda hukumomi da ma'aikatun gwamanati suka rinka karkatar da kudadden da ya kamata a ce sun sanya a asusun gwamnati domin yi wa talakawa aiki.

The Central Bank of Nigeria was established by the CBN Act of 1958 and commenced operations on July 1, 1959.[1] Governor: Sanusi Lamido Sanusi Headquarters: Abuja, Nigeria Quelle wikipedia, public domain
Babban bankin Najeriya

Wadanan kudadden da suka zarta Naira triliyan 4 wadanda rahoton ya nuna cewa an karkatar da su ne ta hanyar boyayyen asusun da ma'aikatu 93 daga cikin 108 da ake da su a kasar, sun yi kememe wajen kin bayyanar da shi. Wannan ya nuna karuwar cin hanci da rashawa da ma karkatar da kudadden gwamnati a cikin kasar, saboda zargin kawar da kai da ake yi wajen hukunta masu wannan laifi, lamarin da ya sanya Dr Hussani Abdu na kungiyar Action Aid da ke yakar cin hanci da rashawa bayyana hatsarin da ke tattare da hakan.

epa03046191 (FILE) A file photograph Goodluck Ebele Jonathan, President and Commander-in-Chief of the Armed Forces of the Federal Republic of Nigeria speaks during the general debate at the 66th session of the United Nations General Assembly at United Nations headquarters in New York, New York, USA, on 21 September 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/JASON SZENES *** Local Caption *** 00000402928322 +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

‘'Yace irin wannan yakan sa tattalin arziki ya tabarbare ne domin alamar ci gaban kasa shine raguwar talauci da rashin aikin yi, muddin talauci da rashin aikin yin ke karuwa to sa a ce wannan ba ci gaba bane. Kuma za ka ga a ko yaushe kasar yanayin ci gaba da na tattalin arziki a kullum tabarbrewa yake yi''.

Bayyanar irin wadnnana rahotanni na tafka mumunan cin hanci da rashawa a tsakanin mutanen da aka damkawa amanar kasa a Najeriya na neman zama dan kullum, daga na sashin man fetir zuwa ga ilimi da ma aikin hanya, rahotanni da suke a gaban gwamnatin domin jiran daukan matakin hukunta wadanda ake zargi domin zama darasi ga na baya.

Eagle Square.jpg
Sakatariyar ma'aikatun gwamnatin Tarayya ta AbujaHoto: DW

Koda yake gwamnati ta dade da ikirarin daukan mataki na ba sani ba sabo a kan matsalar cin hanci da rahsawa da ke zama daya daga cikin babbar matsalar da ke addabar alummar Najeriyar da ma zama abinda ke wa kasar tarnaki na samun ci gaba, to sai dai ga Dr Hussani Tukur masani a fanin ci gaban kasa na mai kashedin cewa.

‘'Duk wani tsari na ci gaba da za'a yi kowane iri ne idan su wadanan mutanen da Alllah ya dorawa hakin yin adalci a tsakanin jama'a ba za su yi ba to, wannan ci gaba ba zai samu ba, ba kuma za'a taba tunane wani ci gaba na kwarai ba. Babau inda za'a ce babu adalci mutane su kwanta su ce sun yarda da rashin adalci, wannan na iya kawo tashin hankali da kuma rashin yarda da lamura da zai sa mutane su dau hukunci a hannunsu, wannan na nuna al'ammura na dada tabarbarewa''.

A yayinda kwamitocin bincike ke ci gaba da bankado zargin aikata halin beraye da ake yi wa jami'an gwamnati da aka baiwa amanar kasa da ma wasu yan kasuwa fiye da na kowace gwamnatin da aka yi a Najeriyar, al'umma na ci gaba da zuba idon ganin mataki na hukunci da gwamnatin za ta dauka a kan wannan matsala da ka iya yin tasiri sosai a yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Mawallafi: Uwaisu Abubakar Idris

Edita: Usman Shehu Usman