1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Ghana jam'iyar NPP ta shigar da kara a kotu

Usman ShehuDecember 28, 2012

Babbar jam'iyar adawan kasar Ghana wato NPP, ta shigar da kara a kotu ta na kalubalantar zaben shugaba John Mahama

https://p.dw.com/p/17AvJ
Ruling party presidential candidate Nana Akufo-Addo gestures as he discusses election results being shown on a TV in his office, in Accra, Ghana Tuesday, Dec. 9, 2008. Official results, which were still being tallied on Tuesday, showed Akufo-Addo with a narrow lead over his main rival, opposition candidate John Atta Mills. (AP Photo/Rebecca Blackwell)
Nana Akufo-Addo, madugun adawa a kasar GhanaHoto: AP

Babbar jam'iyar adawa a kasar Ghana ta shigar da kara a kutu, inda take kalubalantar zaben da ya baiwa shugaba John Mahama nasara. A karar da jam'iyar NPP ta shigar a kotun kolin kasar, ta yi zargin cewa an tabka magudi a zaben ya gabata. Mahama ya samu nasarar sama da kashi 50 cikin dari a yawan kuri'un da aka kada, kamar yadda hukumar zaben kasar Ghana ta sanar. Inda hukumar tace madugun yan adawa Nana Akufo-Addo ya zo na biyu da sama da kuri'u kashi 47 cikin dari. Kasar Ghana mai yawan al'umma miliyan 25 itace ake ganin daya daga kasashen Afirka kalilan da ke dan tsarin demokradiyya mai inganci a Afirka.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi