A Burkina Faso an yi jana′izar mazajen da suka fadi a fagen dagga | Labarai | DW | 02.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Burkina Faso an yi jana'izar mazajen da suka fadi a fagen dagga

Dubban jama'a tare da hukumomi sun gudanar da jana'izar mazajen da suka mutu a lokacin zanga-zagar da ta share gwamnatin Blaise Compaore.

Jama'ar waɗanda suke riƙe da juna hannu da hanu a ciki har'da shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Michel Kafando tare da fira ministan Lt. Col. Isaac Zida.Sun taru a wani dandali da aka sake farfaɗo da sunansa tun lokacin mulkin Thomas Sankara wato danalin juyin juya hali.

Inda daga can ne aka ɗauki gawarwakin mamanta a cikin wata motar soji zuwa maƙabarta.Mutane 24 suka mutu a zanga-zangar da aka yi a ƙarshen watan Oktoban jiya a ƙasar ta Burkina Faso