A ƙasar Masar tarzuma na ƙara bazuwa | Labarai | DW | 08.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A ƙasar Masar tarzuma na ƙara bazuwa

An samu tashe-tashen hankula a yankunan Isma'iliya da Sinai, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Egyptian Muslim brotherhood and supporters of ousted president Mohamed Morsi block the road during clashes with riot police along Ramsis street in downtown Cairo, on October 6, 2013. At least 28 people were killed in clashes between Islamists and police in Egypt, most of them in Cairo, a senior health ministry official said, as thousands of supporters of the military marked the anniversary of the 1973 Arab-Israeli war. AFP PHOTO / AHMED GAMEL (Photo credit should read AHMED GAMEL/AFP/Getty Images)

Hotunan tarzuma a birnin Alƙahira

Wani da ake zargi mai taɗa ƙayar baya ne ya hallaka mutane aƙalla tara a birnin Isma'iliyan ƙasar Masar, kwana guda bayan arangamar jami'an tsaro da masu adawa da juyin mulki ta yi sanadiyar mutuwar mutane dadama. Kazalika wani bam da aka ɗana cikin mota ya hallaka mutane uku kana ya jikkata wasu dadama a yakin Sinai. Fatan kawo ƙarshen tarzuma ya bi ruwa bayan da aƙalla aka hallka ma goya bayan Muhammed Mursi 50, biyo arangamar jami'an tsaro da masu adawa da juyin mulki. Tun bayan kifar da gwamnati Mohammed Mursi magoya bayansa suke tada ƙayar baya. Rikicn baya-bayannan dai ya ɓarke ne a lokacin da 'yan sanda suka yi amfani da ƙarfi don kawar da sansanoni biyu da magoya bayan Mursi suka kafa, a lokacin bikin cika shekaru 40 bayan yaƙin Isra'ila da ƙasashen Larabawa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu