A ƙasar Mali 'yan tawayen sun fara rusa gadoji
January 25, 2013Yan tawayen ƙasar Mali sun rusa wata gada wanda ke da mahimmaci a yaƙin ƙasar. Gadar wanda yan tawayen suka rusa, itace ta haɗe tungar yan tawayen a birnin Gawo da birnin Bamako, kuma itace dakarun ƙasashen waje za su iya bi cikin sauƙi, don kai ga birnin Gawo dake hannun yan tawayen. Rohotanni suka ce a daren jiya yan tawaen suka rusa gadar Tassiga wanda ke kilo mita 95 daga kan iyakar Jamhuriya Nijar da Mali, kana tana kilo mita 150 kacal daga Bamako babban birnin ƙasar Mali. Dama can an tura dakarun jamhuriyar Nijar 500 da na ƙasar Chadi 2000, domin su bude wani fagen daga ta gabacin Mali. Wani direba Abdou Maiga wanda yaga gadar da aka rusa, yace yanzu babu wanda zai fito daga Nijar ya tafi Gao ta wannan hanyar. An dai rawaito jami'an tsaro a jamuhrioyar Nijar na cewa, har yanzu akwai wata doguwar hanya da za iya zagyowa don isa birnin Gao sai da kam tana da ɗan karen nisa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu