Aƙalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a Bama | Labarai | DW | 25.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aƙalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a Bama

Mabiya addinin musulunci 'yan ƙabilar Rohingya na fuskantar barazana da tsangwama a ƙasar Bama.

Wani rikicin da ya kunno kai a ƙasar Bama, ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 20. Wannan rikicin dai ya biyo bayan wasu sabbin tashe tashen hankullan da suka wakana tsakanin mabiya addinin Buddah 'yan ƙabilar Rakhine da kuma mabiya addinin musulunci da akasararinsu daga ƙabilar Rohingya ne wadanda kuma wani rahoton majalisar dinkin duniya suka bayana a matsayin kabilar da ta fi fuskantar wariya da tsangwama a duniya. Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake yawaita samun rikice rikicen tsakanin mabiya addinan biyu a ƙasar ta Bama. Ko a watan Yunin da ya gabata, sama da mutane 105 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hargitsi. Tuni kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta kira hukumomin ƙasar da su ɗauki matakin kawo ƙarshen wannan rikicin.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Umaru Aliyu