Ɗan adam na haddasa ɗumamar yanayi | Labarai | DW | 27.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɗan adam na haddasa ɗumamar yanayi

Masana kimiyya sun ce ta ayyukan da ɗan adam ke yi, yana haddasa ɗumamar yani wanda ke da illa sosai ga al'umma, kuma lamari ne da ya kamata a shawo kan shi tun bai wuce gona da iri ba

Kwamitin da ke kula da lamuran da suka shafi yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya gamsu da cewa ɗan adam ne ke janyo ɗumamar yanayin da ke da illa ga la'umma kuma ya yi hasashen cewa ɗumamar yanayin zai ƙaru daga ƙasa da sifili zuwa maki huɗu da ɗigo takwas bisa ma'aunin Celcius a wannan ƙarnin.

Yanayi mai zafi, da ambaliyar ruwa da fari da tumbatsar teku, na daga cikin barazanar da zasu ƙara ta'azara lamarin, bisa bayanan da hukumar hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci kan sauyin yanayin ta yi a wani rahoton da ta wallafa yau a birnin Stockholm na ƙasar Sweden.

Masu fafutukar kare muhalli, da masana kimiyya, da jagororin siyasa sun ce wannan rahoton da aka daɗe ana jira ya tabbatar da cewa dole ne a daina ƙona abubuwa cikin gaggawa.

A rahoton da ƙungiyar wadda ta taɓa samun lambar yabo na Nobel fitar, ta ce kashi 95 cikin 100 na matsalolin, ɗan adam ne ke kawowa, kuma wannan adadi ya ƙaru da kashi biyar daga rahoton da hukumar ta fitar a shekarar 2007

Wannan ne rahoto na farko cikin jerin rahotanni ukun da ya kamata a fitar wanda ke bitar duk illolin sauyin yanayi kuma manazarta sun bayyana sakamakon da wannan rahoto ya gabatar a matsayin babban barazana ga ƙasashen duniya.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh