Ɓarkewar annobar Polio a Somaliya | Labarai | DW | 16.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓarkewar annobar Polio a Somaliya

Rahotanni sun ce an sami ɓarkewar annoba ta cutar Polio a Somaliya bayan an yi shekaru shidda ana tunani an yi nasarar daƙile cutar a ƙasar

Ein Junge aus Lagos (Nigeria) erhält eine Polio-Impfung (Archivfoto vom 17.09.2005). Jedes vierte Baby auf der Welt bekommt nach Aussage von UNICEF keinen ausreichenden Impfschutz. Besonders betroffen seien Länder in Afrika südlich der Sahara und in Südasien, teilte das Kinderhilfswerk der Vereinten Nationen am Donnerstag (29.09.2005) in Köln mit. Jährlich sterben deshalb zwei Millionen Menschen, 1,4 Millionen von ihnen Kinder, an vermeidbaren Krankheiten wie Masern, Diphtherie, Keuchhusten, Tetanus oder Kinderlähmung. Foto: Onome Oghene (zu dpa 0320) +++(c) dpa - Report+++

Masu aikin agaji a Somaliya na ƙoƙarin daƙile ɓarkewar annobar cutar Poliyo, a yayin da rashin tsaro ke ƙoƙarin janyo musu cikas, kamar yadda wata majiyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana ranar juma'a.

Yau shekaru shidda ke nan rabon Somaliya da wannan cutar inda hukumomin lafiya suka ba da tabbacin cewa an yi nasarar daƙile cutar ta Poliyo a ƙasar baki ɗaya, amma kuma a yanzu an gano mutane aƙalla 105 waɗanda ke ɗauke da ƙwayar cutar abin da ofishin kula da harkokin agajin bil adama na duniya, ya kwatanta a matsayin annoba mafi muni a tarihin ƙasar, kasancewar a ko a bara mutane da suka kamu da cutar a duk faɗin duniya basu kai 250 ba.

Wannan gargaɗi na zuwa ne wuni biyu bayan da ƙungiyar agajin likitoci ta Medecin Sans Frontier ta sanar da cewa za ta dakatar da ayyukanta a ƙasar bayan da ta shafe fiye da shekaru 20 tana kula da marasa lafiya, kuma wannan mataki na ta zai shafi talakwan ƙasar sosai.

Ƙungiyar ta MSF ta ce tana janye ayyukan na ta ne saboda rashin tsaro da kuma irin hare-haren da ake kai mata.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman